Ana tsakiyar Batun El Rufai, Peter Obi Ya Sa Labule da Gwamna Bala kan Dalilai Masu Karfi
Bauchi - Ɗan takarar shugaban kasa a zaɓen 2023 karkashin inuwar jam'iyyar LP, Mista Peter Obi ya kai ziyara ta musamman jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabas.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Peter Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra ya shiga ganawar sirri yanzu haka da Gwamna Bala Mohammed a gidan gwamnatin Bauchi.

Asali: Twitter
Jaridar Channels tv ta tattaro cewa har kawo yanzu babu wata sanarwa kan maƙasudin wannan ziyara ta Obi amma ana hasashen dalilai ne masu ƙarfi.
Sai dai ana tsammanin Peter Obi da gwamnan Bauchi za su yi wa manema labarai jawabi bayan sun fito daga taron wanda ke gudana a sirrance yau Alhamis, 13 ga watan Maria, 2025.
Ku saurari ƙarin bayani...
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng