"Jonathan Ya Yi Bankwana da Siyasa," PDP Ta Magantu kan Fito da Shi 'Dan Takara
- Jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewa babu kamshin gaskiya a batun da ke cewa tana kokarin dawo da Goodluck Jonathan ya tsaya takara
- An samu rahotanni da ke nuna cewa wasu daga cikin ‘yan siyasa a Arewa su na da ra’ayin a tsayar da Jonathan takarar mulkin Najeriya a 2027
- A tattaunawarsa da Legit, mataimaki na musamman ga shugaban PDP na kasa kan yada labarai, Yusuf Dingyadi, ya yi karin bayani kan batun
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja — Jam’iyyar hamayya ta PDP ta yi watsi da rade-radin cewa ana kokarin lallaba tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan, ya sake neman kujerar a zaben 2027.
Yusuf Dingyadi, babban mataimaki na musamman kan yada labarai da sadarwa na shugaban PDP na kasa, Ambasada Umar Damagum, ne ya karyata wannan batu a tattaunawarsa da Legit.

Kara karanta wannan
Bayan rasa El-Rufai, gwamnatin Tinubu ta fadi dan takarar shugaban kasa da zai dawo APC

Asali: Facebook
Bayanin na zuwa duk da gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya ce zai dakatar da aniyar neman kujerar, idan Jonathan zai sake tsaya wa takara, kamar yadda Daily Trust ta wallafa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai makusantan Jonathan sun ce tsohon shugaban ya fi mayar da hankali kan abubuwan da suka shafi ci gaban kasa, ba batun zaben 2027 ba.
PDP ba ta shirin tsayar da Jonathan takara
Yusuf Dingyadi ya bayyana cewa Goodluck Jonathan da kansa ya ce ba shi da wata aniyar sake neman takara ko a dama da shi a siyasar da ke gudana a kasar nan.
A kalamansa:
“Goodluck Jonathan yanzu yana aiki ne a matsayin mai shiga tsakani a kasashen Afirka. Maganar siyasa a Najeriya, ina ganin kamar ya yi bankwana da ita.”
“Ba shi da bukatar tsayawa takara, ba shi da bukatar nuna goyon bayan wata jam’iyya.
Duk da yake an san shi dan jam’iyyar PDP ne, kuma a cikinta ya ci zaben shugaban kasa, wasu na ganin cewa ya yi watsi da abin da ya shafi jam'iyyar. Domin an yi taruka masu muhimmanci da ya dace ya halarta, amma bai je ba.”

Kara karanta wannan
Manyan 'yan siyasar Arewa sun fara lallaba Jonathan, ana son ya nemi kujerar Tinubu
Jonathan na yi wa jam'iyyar PDP kallo na daban
Yusuf Dingyadi ya bayyana cewa kamar yadda tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo, ke kallon PDP, haka Goodluck Jonathan ke kallon jam'iyyar.

Asali: Facebook
Ya ce yadda ‘yan Najeriya ke daukar tsofaffin shugabannin biyu a matsayin ‘yan PDP bai yi daidai da yadda su kansu ke kallon jam’iyyar ba.
Dingyadi ya ce:
“In kun tuna a baya, Goodluck Jonathan ya fito fili ya ce abin da yake takama da shi, shi ne nemawa Najeriya hadin kai, ba maganar siyasa ba.”
PDP: Ana son tsayar da Jonathan takara
A baya, kun samu labarin cewa wasu daga cikin manyan ‘yan siyasar Arewacin Najeriya sun nuna rashin goyon baya ga salon mulkin shugaban kasa a jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu daga cikin manyan ‘yan siyasar na ganin akwai bukatar a lallaba tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya fito takara a inuwar jam’iyyar PDP.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng