2027: Majalisa za Ta Kafa Hukuma domin Maye Gurbin INEC wajen Wasu Ayyuka
- Wani kudiri na neman kafa hukuma mai zaman kanta don yin rijista da sa ido kan jam’iyyun siyasa ya tsallake karatu na biyu a majalisar tarayya
- Kudirin da Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, da dan majalisa Marcus Onobun, suka dauki nauyi, na nufin kwace wannan iko daga INEC
- 'Yan majalisar da suka gabatar da kudirin sun ce matakin zai taimaka wajen tabbatar da gaskiya da rikon amana a harkokin siyasa da zabe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Majalisar wakilai na shirin daukar matakin cire wa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ikon yin rijista da sa ido kan jam’iyyun siyasa a Najeriya.
Wani kudiri da Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, da Marcus Onobun suka gabatar ya tsallake karatu na biyu a zauren majalisa.

Kara karanta wannan
Magana ta ƙare, Kotun Ƙoli ta yanke hukunci kan ƴan Majalisa 27 da suka 'koma' APC

Asali: Facebook
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa kudirin na neman kafa wata hukuma mai zaman kanta wacce za ta maye gurbin INEC wajen yin rijista da lura da harkokin jam’iyyun siyasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisa za ta rage nauyi ga hukumar INEC
Yayin kare kudirin a zaman majalisar, Marcus Onobun ya ce matakin zai bai wa INEC damar mayar da hankali kan gudanar da zabuka.
A cewarsa, yin rijista da kula da jam’iyyun siyasa abu ne mai nauyi da ke hana hukumar INEC gudanar da zabuka yadda ya kamata.
Ya kara da cewa:
“Al’ummar Najeriya da dama na ganin cewa tsafta da amana a zabuka na da nasaba da yadda ake yin rijista da gudanar da jam’iyyun siyasa.”
Sabuwar hukumar da za a kafa don aikin
Sabon kudirin yana shirin kafa wata hukuma don yin rijistar jam’iyyu da sanya ido kan kudin shigar su.

Kara karanta wannan
Majalisar shari'ar Musulunci ta goyi bayan rufe makarantu, ta kirayi jihohi 3 su bi sahu
Haka nan, kudirin ya tanadi kafa wata kotu da za ta rika warware rigingimu tsakanin ‘yan jam’iyya don kauce wa rikice-rikicen siyasa.
Hon. Onobun ya bayyana cewa:
“Don tabbatar da ingantacciyar dimokuradiyya, wajibi ne a kafa hukuma mai zaman kanta da za ta sa ido kan jam’iyyun siyasa.”
Majalisar wakilan tarayya ta amince da kudirin
Bayan gabatar da kudirin, an kada kuri’ar amincewa da shi a zaman majalisa, inda shugaba Tajudeen Abbas ya amince da ci gaba da tattauna shi.
An bayyana cewa sabuwar dokar za ta samar da hukunci ga jam’iyyun da suka saba ka’ida domin tabbatar da tsari mai inganci.
Onobun ya bukaci ‘yan majalisa da su mara wa kudirin baya, yana mai cewa:
“Idan har muna son ceton dimokuradiyyarmu, lokaci ya yi da za mu dauki mataki.”
A yanzu haka dai za a jira mataki na gaba da karatu na gaba da majalisa za ta yi a kan kudirin da amincewar majalisar zartarwa kafin ya zamo doka a Najeriya.

Kara karanta wannan
Ana batun cin zarafin Sanata, Remi Tinubu ta bukaci karin wakilcin mata a majalisa

Asali: UGC
Majalisa ta ki yarda da bukatar Natasha
A wani rahoton, kun ji cewa majalisa ta ki amincewa da watsa zaman sauraron korafin da Natasha Akpoti ta mika mata.
Sanata Natasha ta shigar da korafi ne a kan zargin shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio da neman lalata da ita.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng