Zaben Gwamna Ya Kankama: INEC Ta ba Jam'iyyu 19 Wa'adi Su Fitar da 'Yan Takara
- Hukumar INEC ta ba jam'iyyun siyasa wa'adin makonni biyu su gudanar da zabe fitar da gwani domin tunkarar zaben gwamnan Anambra
- Daga cikin jam’iyyu 19 da aka yi wa rijista, 12 sun mika jadawalin zaben fitar da gwaninsu ga INEC, yayin da bakwai suka gaza yin hakan
- INEC ta gargadi jam’iyyu da kada su sauya jadawalin zabensu domin hakan na iya janyo masu matsala da kuma janyo tsadar gudanar da zabe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Anambra - Hukumar zabe ta kasa (INEC) ta ba jam'iyyun siyasa da ke son tsayawa takara a zaben gwamnan Anambra wa'adin makonni biyu su gudanar da zaben fitar da gwani.
INEC ta cimma matsayar bayar da wa'adin ne a taron mako-mako da take yi, wanda aka gudanar a Abuja a ranar Alhamis, 6 ga Maris, 2025.

Asali: Getty Images
INEC ta ba jam'iyyu wa'adin zaben fitar da gwani
Sam Olumekun, kwamishinan INEC kuma shugaban kwamitin wayar da kan masu zabe, ya sanar da hakan, a sanarwar bayan taro da ya fitar, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishin hukumar zaben ya ce:
“Mun nazarci shirye-shiryenmu na zaben gwamna a Anambra. Wannan ya sa muka cimma wasu matsaya game da zaben mai zuwa."
Ya tunatar da cewa INEC ta fadi lokacin zaben gwamnan jihar tun a ranar 13 ga Nuwamba, 2024, wato fiye da kwana 360 kafin ranar zabe, kamar yadda doka ta tanada.
A cewarsa, jam'iyyun siyasa za su gudanar da zaben fitar da gwani daga ranar 20 ga Maris, 2025, zuwa 10 ga Afrilu, 2025, kamar yadda jadawalin zabe ya tanada.
Anambra: INEC ta gargadi jam'iyyu gabanin zabe
Daga cikin jam’iyyu 19 da aka yi wa rijista, 12 sun riga sun mika jadawalin zaben fitar da gwaninsu ga INEC, a cewar Sam Olumekun.
Kwamishinan ya kara da cewa:
“Mun amince a taronmu da jam’iyyun siyasa a Janairu cewa bayar da jadawali da wuri zai taimaka mana wajen ingantaccen sa-ido kan zaben."
Ya bukaci sauran jam’iyyu bakwai da suka gaza mika bayanansu su gaggauta yin hakan domin gujewa matsaloli a nan gaba.
Hukumar ta jaddada bukatar jam’iyyu su bi jadawalin da suka mika ba tare da sauya rana ko wurin zabe ba.

Asali: Getty Images
INEC ta shirya gudanar da sahihin zabe a Anambra
“Canza jadawalin zaben fitar da gwani ba tare da sahalewar hukuma ba na kawo cikas ga aikin INEC da kuma tsadar gudanar da zabe,” in ji Olumekun.
Ya ce irin wadannan canje-canje na janyo matsaloli wajen tura jami’an sa-ido da kuma kawo cikas ga shirin zaben gaba daya.
INEC ta bukaci jam’iyyun siyasa su bi ka’idojin dokar zabe don gujewa matsaloli da ka iya hana gudanar da sahihin zabe a jihar anambra.
Kwamishinan INEC ya jaddada cewa:
“Mun kuduri aniyar gudanar da sahihin zabe mai cike da adalci. Muna bukatar hadin kan jam’iyyun siyasa da masu ruwa da tsaki."
Zaben gwamna na Anambra zai gudana ranar 8 ga Nuwamba, 2025, tare da sa ido daga hukumomi da masu lura da harkokin zabe.
Duba sanarwar da INEC ta fitar a shafinta na X game da wannan umarni a kasa:
Anambra: PDP ta fara sayar da fom din takara
A wani labarin, mun ruwaito cewa, jam’iyyar PDP ta fitar da jadawalin zaben gwamnan Anambra, inda ta kayyade Naira miliyan 40 a matsayin kudin fom ɗin takara.
Jam'iyyar ta sanar da cewa zaɓen fitar da gwanin zai gudana a ranar 5 ga Afrilu, yayin da za a tantance ‘yan takara a ranar 11 ga Maris.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng