Zargin Lalata: Sanata Natasha na Tsaka Mai Wuya, Hadimin Osinbajo Ya Tona Shirin Majalisa
- Tsohon mai magana da yawun mataimakin shugaban ƙasa, Laolu Akande ya caccaki abin da ya kira yunkurin yi wa Sanata taron dangi a Majalisa
- Mista Akande ya ce bai kamata Majalisar Dattawa ta rufewa Natasha Akpoti baki ba, a yi bincike na gaskiya don tabbatar da zarginta
- Wannan dai na zuwa ne bayan sanatar ta ƙauracewa zaman kwamitin ladabatarwa na Majalisar dattawan a jiya Laraba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Tsohon kakakin mataimakin shugaban kasa, Laolu Akande, ya bayyana damuwarsa kan abin da ya kira yunkurin rufe bakin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
Sanata Natasha, wadda ke wakiltar Kogi ta Tsakiya a majalisar dattawa, ta zargi shugaban majalisar, Godswill Akpabio da neman cin zarafinta ta hanyar lalata.

Asali: Twitter
Sai dai tuni Sanata Akpabio ya musanta wannan zargi, yana mai cewa bai taɓa cin zarafin mace ba a rayuwarsa, kamar yadda Vanguard ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi wa Natasha taron dangi a Majalisa
A wata hira da ya yi da tashar Channels tv a shirin Sunrise Daily, Akande ya bukaci majalisar dattawa da ta dakatar da abin da ya kira "yi wa Natasha taron dangi."
“Ya kamata su daina wadannan taruka da yunkurin yi wa matar nan taron dangi da matsa mata lamba. Shugabannin majalisa su tabbatar da cewa za a bi lamarin ba tare da son zuciya ba.
“Idan an gama bincike kuma an ga cewa ta saba dokokin majalisa, za a iya daukar matakin da ya dace. Amma wannan dabi’ar da wasu ke nunawa, maza na yaɗa maganganu a kanta ba abu ne mai kyau ba.
“Wannan mace ta fito fili ta bayyana cewa an ci zarafinta. Ya zama wajibi a duba zarginta da kulawa, dole mu kula, majalisar dattawa ta kula, ka da ta yi ƙoƙarin rufe mata baki.
- Laolu Akande.
Majalisar Dattawa ba ta kyauta ba
Tsohon hadimi a fadar shugaban ƙasan ya ce kowa na ganin yadda ƴan Majalisar Dattawa maza ke gudanar da taruka suna maganganun ƙasƙanci a kanta.
“A halin yanzu, abin da muke gani shi ne, maza ne kawai ke gudanar da taruka, suna magana, suna fitowa kafafen yada labarai suna kokarin kaskantar da ita.
"Wannan ba kyakkyawar ɗabi'a ba ce ga majalisar dattawa ta Najeriya,” in ji Akande.

Asali: Facebook
Natasha ta ƙi halartar zaman kwamitin ladabtarwa
A ranar Laraba, 5 ga watan Maris, 2025, Sanata Natasha ta ƙauracewa halartar zaman kwamitin ladabtarwa, wanda ke gudanar da bincike kan zargin da ake mata na karya doka.
Shugaban kwamitin, Sanata Neda Imaseun, ya nuna takaicinsa kan rashin halartar ta.
“Mun jira har na tsawon awa daya, amma har yanzu ba ta zo ba. Ina fatan kafin mu kammala wannan zama, za ta halarta,” in ji shi.

Kara karanta wannan
Zargin lalata: Sanata Natasha ta fitar da saƙo mai zafi bayan dakatar da ita a Majalisa
Amma a cewar Laolu Akande, duk wannan wani yunƙuri ne na rufe mata baki, wanda bai dace da ƙimar Majalisar Dattawan Najeriya ba.
An tura wasika ga Sanata Akpabio
A wani labarin, kun ji cewa masu ruwa da tsaki a Kogi ta Tsakiya sun nuna danuwa kan rigimar da sanata mai wakiltarsu ta kinkimo a Majalisar dattawa.
Bisa haka ne ƙungiyar masu ruwa da tsakin ta rubuta buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga shugaban Majalisar Dattawa, inda ta yi barazanar yi wa Natasha Akpoti kiranye.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng