Zargin Shugaban Majalisa da Neman Lalata da Matar Aure Ya Riƙide, An Samu Wasiƙa daga Kogi

Zargin Shugaban Majalisa da Neman Lalata da Matar Aure Ya Riƙide, An Samu Wasiƙa daga Kogi

  • Masu ruwa da tsaki a mazaɓar Kogi ta Tsakiya sun rubuta wasiƙa zuwa ga shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio
  • A wasiƙar, sun nesanta kansu da halayyar da Natasha Akpoti ta nuna, sun zayyana irin gudummawar da Akpabio ya ba ta
  • A ƙarƙashin kungiyarsu, masu ruwa da tsakin sun buƙaci Majalisar dattawa ta ɗauki matakin ladabtarwa kan Sanata Natasha

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kogi - Ƙungiyar masu ruwa da tsaki a mazaɓar Kogi ta Tsakiya ta nesanta kanta daga rikicin da ke faruwa tsakanin Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da Natasha Akpoti-Uduaghan.

Ƙungiyar mai suna Kogi Central Concerned Stakeholders ta ayyana cikakken goyon bayanta ga Akpabio tare da neman a ɗauki matakin ladabtarwa kan Natasha.

Sanata Natasha da Akpabio.
Masu ruwa da tsakin Kogi ta Tsakiya sun nesanta kansu daga halayyar Sanata Natasha Hoto: @NGRSenate
Asali: Twitter

Hakan na kunshe ne a wata wasiƙa da masu ruwa da tsakin suka aika zuwa ga shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, kamar yadda Daily Trust ta kawo.

Kara karanta wannan

Daga ƙarshe, an ji ta bakin shugaban Majalisa kan zargin neman lalata da Sanata Natasha

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Natasha ta fara fuskantar matsala a Kogi

Ƙungiyar ta bayyana takaicinta kan yadda rikicin ya dauki wani sabon salo da ke barazana ga martabar majalisa.

Ta ce abin da bai wuce matsalar rashin bin doka da oda ba, ya rikide zuwa hari da barazaka ga mutuncin Shugaban Majalisar Dattawa.

Kungiyar ta tuna da irin goyon bayan da Sanata Akpabio ya bai wa Sanata Natasha tun kafin ta zama 'yar majalisa, ta hanyar dangantakar da ke tsakaninsa da mijinta, Emmanuel Uduaghan.

'Shugaban Majalisa ya taimaki Natasha'

Mutanen sun kuma bayyana cewa Shugaban Majalisar ya halarci bikin aurensu tare da sauran manyan mutane, abin da ke nuna irin mutuncin da ke tsakaninsu.

Bugu da kari, kungiyar ta ce Sanata Akpabio ya taka rawar gani wajen tabbatar da cewa Sanata Natasha ta samu damar wakiltar mazabarta.

A cewar wasiƙar ƙungiyar, duk da kasancewarta sabuwar 'yar majalisa, Sanata Natasha ta samu damar shugabantar kwamitin kula da harkokin cikin gida.

Kara karanta wannan

Natasha: 'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga zanga, sun harba barkonon tsohuwa

Akpabio ya gatanta Sanata Natasha

Kungiyar ta ce Natasha ta kuma samu dama ta halartar taruka na kasa da kasa tare da Shugaban Majalisar, har ta dauki hotuna da shi.

"Haka nan, ta sami shirye-shiryen tallafawa jama’a da ta yi amfani da su wajen bunkasa karfinta a siyasa.
Duk da irin wadannan damammaki da Sanata Natasha ta samu, mun yi mamakin yadda lamarin ya rikide zuwa zarge-zargen cin zarafi da suka bazu a kafafen yada labarai," in ji wasiƙar.

Saboda haka, kungiyar ta nesanta kanta daga halayyar Natasha Akpoti-Uduaghan., tana mai cewa kamata ya yi ta mayar da hankali kan wakilcin da aka zabe ta domin yi maimakon janyo rikici.

An yi barazanar yi wa Natasha kiranye

Kungiyar ta yi kira ga Sanata Natasha da ta daina bata sunan mutanen Kogi ta Tsakiya da halayyar da ba ta dace ba, rahoton The Nation.

"Idan haka ta ci gaba da faruwa, za mu fara shirin yi wa Sanata Natasha kiranye," in ji masu ruwa da tsakin.

Kara karanta wannan

Zargin 'neman lalata' ya ƙara girma, Sanata Natasha ta gabatar da takarda a Majalisa

Natasha.
An fara barazanar yi wa Sanata Natasha kiranye Hoto: Natasha Akpoti-Uduaghan
Asali: Original

A karshe, kungiyar ta tabbatar wa Shugaban Majalisar Dattawa cewa suna tare da shi da sauran ‘yan majalisa.

Sannan ta yi kira ga majalisar da ta dauki matakin ladabtarwa domin zama izina ga sauran ‘yan majalisar da ka iya aikata irin hakan nan gaba.

Akpabio ya yi magana kan zargin lalata

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Godswill Akpabio ya karyata zargin neman lalata da Natasha, ya ce bai taɓa cin zarafin mace ba a rayuwarsa.

Shugaban Majalisar ya bayyana cewa tun ranar 25 ga Fabrairu ya fara karɓar kira daga mutane da dama dangane da zargin da aka yi masa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262