Ana Zargin An Lakadawa Hadimin Tsohon Gwamna Duka kan Sukar Sanatan Jigawa

Ana Zargin An Lakadawa Hadimin Tsohon Gwamna Duka kan Sukar Sanatan Jigawa

  • Rahotanni sun ce an lakada wa hadimin tsohon gwamnan Jigawa, Badaru Abubakar duka bayan ya soki wani sanata a rediyo
  • Mutumin mai suna Habibu Muhammad ya zargi Sanata Babangida Husseini da gazawa wajen wakiltar mazabarsa a majalisar dattawa
  • An ce masu dukansa sun bukaci ya daina sukar mai gidansu, inda suka ce yana cin mutuncin shugabanni babu gaira-babu dalili
  • Muhammad ya ce an yi yunkurin kashe shi saboda siyasa, kuma ya bukaci hukumomi su dauki mataki domin kare lafiyarsa nan gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Dutse, Jigawa - Ana zargin an lakadawa wani tsohon hadimin gwamnan Jigawa, Muhammad Badaru duka bayan ya soki Sanata Babangida Husseini a wani shiri na gidan rediyo.

Habibu Muhammad ya zargi sanatan da gazawa wajen wakiltar mazabarsa a majalisa, ya bukaci jam'iyyar APC ta canza shi a zaben 2027 domin inganta rayuwar al'umma.

Kara karanta wannan

Mataimakiyar gwamna ta ji wuta, ta yi murabus daga muƙaminta? Bayanai sun fito

Yadda aka daka tsohon hadimin Badaru a Jigawa
Wasu da ake zargin magoya bayan wani Sanata ne sun yi wa tsohon hadimin Badaru duka. Hoto: Governor Badaru Abubakar.
Source: Facebook

A wani faifan bidiyo da aka wallafa a kafafen sada zumunta da Premium Times ta samu, wasu mutane hudu sun buge shi tare da cewa yana cin mutuncin jagororin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mohammed Badaru Abubakar shi ne ke riƙe da muƙamin Ministan tsaro a Najeriya bayan Bola Tinubu ya nada shi domin kakkabe yan bindiga musamman a yankin Arewacin Najeriya.

Badaru ya sha alwashin dakile matsalolin tsaro

A baya, Legit Hausa ta ruwaito muku yadda ministan tsaron ya sha alwashin kawo karshen matsalar tsaro nan ba da jimawa ba.

Badaru ya ce da zarar gwamnati ta samar da kayan aiki na zamani ga jami'an tsaro to shikenan kasar za ta yi bankwana da rashin tsaro.

Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne yayin taron Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya, NBA a Abuja inda ya fadi kokarin da su ke yi na tabbatar da haka.

An yi wa tsohon hadimin Badaru dukan tsiya a Jigawa
Wasu yaran Sanata sun yi wa tsohon hadimin Badaru duka saboda sukar mai gidansu. Hoto: Defence Headquarters Nigeria.
Source: Facebook

Ana zargin yaran Sanata da dukan dan siyasa

Kara karanta wannan

Neman lalata: Majalisa ta yi watsi da bukatar Natasha kan zargin Akpabio

Habibu Muhammad ya bayyana cewa an cire wani sashe na bidiyon, inda aka nemi ya karbi N10m domin daina sukar sanatan saboda rayuwarsa.

Ya ce an yi yunkurin kashe shi saboda bambancin siyasa, yana mai bukatar hukumomi su dauki mataki kan wadanda suka kai masa hari domin yi musu hukunci daidai da laifinsu.

Muhammad ya ambaci sunayen mutanen da suka farmake shi, yana zargin sanatan da yin amfani da su don razana shi da kuma neman hana shi fadin albarkacin bakinsa.

Sanata Babangida Husseini bai amsa kiran da aka yi masa don jin ta bakinsa kan zargin da Muhammad ke yi masa ba na shan duka daga wasu daga cikin mukarrabansa.

Badaru ya fadi dalilin ba shi Minista

A baya, kun ji cewa Ministan tsaron a Najeriya, Mohammed Badaru Abubakar ya taɓo batun muƙamin da ya samu a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Mohammed Badaru ya bayyana cewa rawar da ya taka a lokacin da yake mulkin jihar Jigawa, ta taimaka masa wajen samun muƙamin.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa hanyoyin da ya bi wajen samar da tsaro a Jigawa na taimaka masa a yanzu da yake kan ministan tsaron Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.