Tirƙashi: PDP Ta Kori Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, An Fadi Zunubinsa
- Kwamitin gudanarwar PDP a Abia ya sanar da korar Sanata Adolphus Wabara bisa zargin cin amanar jam’iyya da goyon bayan LP
- A kwanakin baya, PDP ta dakatar da Wabara, amma jam’iyyar a matakin kasa ta soke wannan dakatarwa ta bakin Debo Ologunagba
- Sai dai PDP a Abia ta sake korar shugaban BoT na kasa bayan nazarin rahoton kwamitin ladabtarwa, bisa tanadin dokokin jam’iyyar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abia - Kwamitin gudanarwa (SWC) na PDP a jihar Abia ya sanar da korar tsohon shugaban majalisar dattawa, Adolphus Wabara, daga jam’iyyar an take.
Shugaban PDP na jihar, Elder Abraham Amah, ya ce an kori Wabara ne saboda cin amanar jam’iyya da aikata ayyukan da suka saba manufofin PDP.

Asali: Twitter
Laifin da Wabara ya yi PDP ta kore shi
Elder Amah ya bayyana cewa Wabara ya yi laifi ta hanyar goyon bayan sake zaɓen gwamnan Abia na jam’iyyar LP a wa’adi na biyu, inji rahoton The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Korar na zuwa ne duk da Wabara ya ce bai yi magana da yawun PDP ba, sai dai a matsayinsa na ɗan Najeriya mai ‘yancin fadin albarkacin baki.
Idan ba a manta ba, mun ruwaito cewa PDP ta jihar Abia ta dakatar da Wabara, wanda shi ne shugaban kwamitin amintattunta (BoT).
Sai dai tun ba a je ko ina ba, jam'iyyar APC a matakin kasa ta soke wannan dakatarwa da aka yi wa Wabara ta bakin kakakinta, Debo Ologunagba.
PDP ta sake korar Wabara bayan rahoton kwamiti
A ranar 25 ga Fabrairu, 2025, SWC ta nazarci rahoton kwamitin ladabtarwa (DC) kan zargin cin amanar jam’iyya da ake yi wa Wabara.
Bayan cikakken bincike, SWC ta amince da shawarwarin kwamitin, ta yanke hukuncin korar Wabara daga PDP bisa tanadin dokokin jam’iyya a ranar Talata.
Sanarwar kwamitin gudanarwar ta ce matakin ya dace da sashe na 57(3) da 59(1) na kundin tsarin mulkin PDP na 2017 da aka yi wa garambawul.
Ana so PDP ta nada sabon shugaban BoT

Asali: Facebook
Kwamitin ya bukaci PDP ta kasa ta nada sabon shugaban rikon kwarya na kwamitin amintattu (BoT) domin ci gaba da tafiyar da jam’iyyar.
Sanarwar, wacce Elder Abraham Amah da Chief Peter Nwaokonko suka sanya hannu, ta jaddada bukatar bin dokokin jam’iyyar PDP.
Amah ya ce PDP a jihar Abia za ta ci gaba da ladabtar da duk wanda ya karya doka domin kiyaye hadin kai.
Wabara ya garzaya kotu don hana dakatar da shi
To sai dai, wata kotun jihar Abia da ke Obehie ta dakatar da Elder Amah daga aiwatar da hukuncin dakatarwar Wabara daga jam’iyyar PDP.
Wabara ya ne da kansa ya shigar da ƙarar mai lamba HUK/8/2025, yana neman kotun ta hana Amah aiwatar da hukuncin dakatarwarsa daga PDP.
Har yanzu ana jiran matakin da PDP ta kasa za ta sake dauka kan hukuncin korar Wabara a karo na biyu, yayin da ra’ayoyi daban-daban ke ci gaba da bayyana.
BoT: PDP ta tabbatar da nadin Wabara
A wani loabarin, mun ruwaito cewa, jam'iyyar PDP ta tabbatar da tsohon shugaban majalisar dattawa, Adolphus Wabara, a matsayin shugaban kwamitin amintattu na kasa (BoT).
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmad Makarfi ya zama sakataren BoT na PDP a wani taron kwamitin karo na 76 da aka gudanar a birinin tarayya Abuja.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng