Alamar Rauni ne: Tsohuwar Sanata Ta Dura kan Natasha game da Zargin Akpabio
- Sanata Florence Ita-Giwa ta ce matan da suka zama sanatoci ba za a iya cin zarafinsu ba, tana sukar ikirarin Natasha Akpoti-Uduaghan
- Akpoti-Uduaghan ta ce Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya hana ta gabatar da kuduri saboda ta ki yarda da bukatarsa ta lalata
- Ita-Giwa mai shekaru 79 ta ce idan mace ta zama sanata, ba za ta koka da cin zarafi ba, domin tana da matsayi daya da maza a majalisa
- Tsohuwar sanatar ta ce mata ba su da wata bukata da za ta sa su yi korafi kan cin zarafi, domin samun nasarar zabe yana nuna karfinsu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Tsohuwar mai ba shugaban kasa shawara, Sanata Florence Ita-Giwa ta yi magana kan iƙrarin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
Sanata Ita-Giwa ta ce ba za a iya cin zarafin mata da suka zama sanatoci ba duba da matsayinsu a cikin majalisa.

Asali: Twitter
Zargin da Sanata Natasha ke yi wa Akpabio
A wata hira da ita a Arise TV ranar Talata, 4 ga Maris, 2025, Ita-Giwa ta ce mata ba za su ce an ci zarafinsu a majalisa ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya biyo bayan zargin da Natasha take yi wa Akpabio cewa yana fatali da kudurorinta ne saboda ta ki amincewa ya yi lalata da ita.
Natasha ta bayyana yadda Akpabio yake neman lalata da ita tun wata ziyara da ta kai masa a gidansa inda ya yi mata alkawarin ba ta fifiko idan ta amince masa.
'Korafin Natasha alamar rauni ne'.- Sanata Ita-Giwa
Ita-Giwa ta ce muƙamin sanata ga mace ya wuce a ci zarafinta saboda a majalisa mata da maza dukansu daya ne.
Tsohuwar sanatar ta ce:

Kara karanta wannan
Natasha: 'Yan siyasar Arewa sun huro wuta, suna so shugaban majalisa ya yi murabus
"Idan mace ta zama sanata, ta wuce matakin da za a ce an ci zarafinta, a majalisa, kowa daidai yake."
"Ba na cewa tana karya, amma a wannan matakin siyasa, idan mace ta ce an ci zarafinta, alama ce ta rauni."
Lokacin da aka tambayeta ko mata su yi shiru idan ana cin zarafinsu, Ita-Giwa ta ce yin korafi irin wannan rauni ne ga mace.

Asali: Twitter
Yadda girman Sanatoci mata yake a majalisa
Ta ce:
"Ba na goyon bayan Sanata Akpoti. Idan mace ta fito tana zargin namiji da lalata a wannan matakin, rauni ne."
Ita-Giwa ta jaddada cewa mata sanatoci su dauki kansu daidai da maza, domin samun nasarar zabe ba abu ne mai sauki ba, cewar rahoton Punch.
Sanata Kingibe ta dura kan Natasha
Kun ji cewa Sanata Ireti Kingibe da ke wakiltar Abuja ta yi magana kan zargin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan game da shugaban majalisa, Godswill Akpabio.
Ireti ta ce sau da yawa ana matsar da ‘yan majalisa mata kamar yadda ake yi wa maza, kuma Natasha ta fi kowacce mace samun gata a wurin Godswill Akpabio.
Har ila yau, Sanatar ta ce babu wata daga cikinsu a majalisa da ta fuskanci cin zarafi, kuma Natasha ba ta taba tuntubarsu kan wannan batu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng