PDP Ta Gamu da Nakasu, 'Dan Takarar Gwamna Ya Fice daga Jam'iyya

PDP Ta Gamu da Nakasu, 'Dan Takarar Gwamna Ya Fice daga Jam'iyya

  • Jam'iyyar PDP mai adawa a jihar Legas ta samu koma baya a siyasance bayan ta rasa ɗaya daga cikin manyan jiga-jiganta
  • Tsohon ɗan takararta na zaɓen gwamna a 2023, Dr. Olajide Adeniran, ya sanar da ficewarsa a ranar Litinin, 3 ga watan Maris 2025
  • Olajide Adeniran wanda aka fi sani da Jandor ya bayyana cewa ya fice daga PDP saboda yadda shugabanninta suka ci dunduniyarta
  • Tsohon ɗan takarar gwamnan ya bayyana cewa zai yi shawarwari kafin ya yanke hukunci kan jam'iyyar da zai koma a nan gaba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Legas, Dr. Olajide Adediran, wanda aka fi sani da suna Jandor ya fice daga jam'iyyar PDP.

Olajide Adeniran ya fice daga jam'iyyar PDP wacce ke adawa a jihar Legas ne a ranar Litinin, 3 ga watan Maris 2025.

Kara karanta wannan

Littafin IBB ya tono tsuliyar dodo, an fadi kabilar da ake so ta yi mulki a 2027

Olajide Adeniran ya fice daga PDP
Dan takarar gwamnan PDP a Legas ya fice daga jam'iyyar Hoto: Dr. Olajide Adeniran
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa ya sanar da hakan ne yayin da yake jawabi ga manema labarai, a ofishinsa da ke birnin Ikeja na jihar Legas a ranar Litinin

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jandor shi ne ɗan takarar gwamnan PDP na jihar Legas a zaɓen shekarar 2023 da ya gabata.

Meyasa Jandor ya fice daga PDP?

A cewarsa dalilansa na barin PDP ba su rasa nasaba da rashin ɗa'a da cin dunduniyar jam'iyyar da ake yi, rahoton The Punch ya tabbatar.

Ya bayyana cewa waɗannan abubuwan sun zama ruwan dare a tsohuwar jam'iyyarsa.

Tsohon ɗan takarar gwamnan ya ce ya ɗauki matakin ficewa daga PDP ne saboda wasu abubuwa da jiga-jigan jam'iyyar, ciki har da tsohon mataimakin shugaban PDP na ƙasa, Cif Olabode George suka yi.

A cewar Jandor, waɗannan shugabanni sun yi aiki domin rashin nasarar PDP a babban zaɓen shekarar 2023.

"Za mu nemi shawarwari sosai kafin mu yanke shawarar komawa zuwa wata jam'iyyar."

Kara karanta wannan

Gwamna ya shiga matsala, Majalisar Dokoki ta ba shi sa'o'i 48 ya bayyana a gabanta

"Abin da yake bayyane a yanzu shi ne mun bar jam'iyyar PDP."

- Dr. Olajide Adeniran

Jandor tsohon 'dan jam'iyyar APC ne

Ƙafin shigarsa PDP, Jandor mamba ne a jam'iyyar APC inda ya jagoranci ƙungiyar Lagos4Lagos Movement, wacce ke fafutukar ganin ana bin tsarin dimokuraɗiyyar cikin gida a APC.

Ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP a watan Janairun 2022, inda daga baya ya samu tikitin takarar gwamna a zaɓen 2023.

A wannan zaɓen, Jandor ya zo a matsayin na uku, ya biyo bayan Gwamna Babajide Sanwo-Olu na APC da Gbadebo Rhodes-Vivour na jam'iyyar LP.

Jiga-jigan PDP sun sauya sheƙa zuwa APC

A wani labarin kuma, kun ji tsohon ɗan takarar gwamna na jam'iyyar AAC da wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP sun sauya sheƙa zuwa APC a Zamfara.

Ɗan majalisar wakilai, Aminu Sani Jaji ne ya tarɓi masu sauya sheƙar zuwa APC a gidansa da ke Gusau, babban birnin Zamfara.

Masu sauya sheƙar sun bayyana cewa sun yanke shawarar komawa APC ne saboda babu jam'iyyar mai ƙarfinta a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng