Me Yake Shiryawa?: Na Hannun Damar Peter Obi da Ya Fice daga LP Ya Gana da Atiku

Me Yake Shiryawa?: Na Hannun Damar Peter Obi da Ya Fice daga LP Ya Gana da Atiku

  • Tsohon kakakin yakin neman zaben LP, Kenneth Okonkwo, ya kai ziyara ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar
  • Kenneth Okonkwo wanda a bara ya fice daga jam'iyyar LP, ya ce Atiku ne ya kira sa domin sun tattauna hanyoyin inganta kasar Najeriya
  • Tsohon na hannun damar Peter Obin ya jaddada cewa ba zai koma APC ko PDP ba, amma yana duba yiwuwar gina sabuwar tafiyar siyasa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon kakakin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar LP, Kenneth Okonkwo, ya kai ziyara ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Jarumin fina-finan na Nollywood, wanda ya kasance mai goyon bayan Peter Obi a baya, ya bayyana dalilin ziyarar a shafukansa na sada zumunta.

Kenneth Okonkwo ya bayyana dalilin ganawa da Atiku Abubakar a Abuja
Atiku Abubakar ya gana da tsohon na hannun damar Peter Obi a Abuja. Hoto: @Tony_Ogbuagu
Asali: Twitter

Tsohon jigon LP ya gana da Atiku Abubakar

A sanarwar da ya fitar a shafinsa na Instagram, ya bayyana cewa Atiku ne ya gayyace shi domin tattauna hanyoyin da za a bi domin inganta Najeriya.

Kara karanta wannan

Tsohon makusancin Peter Obi ya hango rugujewar LP, ya fadi makomarsa a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kennet Okonkwo ya ce:

“Na samu babban gata kuma ina alfahari da ganawata da Atiku Abubakar a wani taron shawara kan yadda za a ceto kasarmu daga halin da take ciki.”

Tsohon dan wasan kwaikwayo kuma dan siyasa ya jaddada cewa halin da Najeriya ke ciki na bukatar hadin gwiwar dukkanin masu kishin kasa domin dawo da martabar kasar.

Okonko ya fice daga jam'iyyar LP

Okonkwo ya bar jam'iyyar LP a bara bayan ya zargi Peter Obi da gaza samar da jagoranci mai karfi da zai iya fitar da Najeriya daga matsalolinta.

A cewarsa, babbar matsalar Najeriya ita ce shugabanci maras inganci da ‘yan siyasar da suka mamaye mulki ta hanyar son zuciya da cin hanci da rashawa.

Ya bayyana cewa, domin kawar da irin wadannan shugabanni, dole ne a samu jam’iyya mai karfi da ke da tushe a kasa, wadda za ta samar da shugabanni nagari.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi magana kan saukar farashin abinci, ya yi alkawarin karin sauki

'Obi ya ba ni kunya' - Kenneth Okonkwo

Kenneth Okonkwo ya yi farin cikin haduwa da Atiku Abubakar
Tsohon jigon LP, Kenneth Okonkwo na murna yayin da ya hadu da Atiku Abubakar. Hoot: @Tony_Ogbuagu
Asali: Twitter

Tsohon kakakin LP ya ce Obi ya ba shi kunya da gazawar da ya yi wajen gina jam’iyyar LP zuwa matakin da za ta iya samar da shugabanci mai nagarta.

Okonkwo ya ce:

“Bayan zaben 2023, ni da sauran ‘yan Najeriya mun sa ran Obi zai dauki matakan karfafa LP.
“Na yi tunanin zai yi amfani da damar da ke hannunsa domin gina jam’iyyar da za ta samu goyon bayan jama’a da kuma iya kwace mulki daga hannun shugabannin da suka gurbata kasa.”

Ya ce duk da hakan, ya ci gaba da kare Obi, yana fata zai dauki matakan da suka dace, amma hakan bai faru ba, wanda ya tilasta shi ficewa daga LP.

Okonkwo: Matakin tsohon jigon LP na gaba

Dangane da matakinsa na gaba, Okonkwo ya bayyana cewa yana kokarin gina sabon tafarkin siyasa amma ba zai koma APC ko PDP ba.

Kara karanta wannan

Littafin IBB: Fitaccen Lauya, Falana zai maka Janar Babangida a kotu, ya jero dalilai

Dan siyasar ya ce:

“Tun bayan ficewata daga jam'iyyar LP, na fara tattaunawa da mutanen da ke da irin tunanina domin tantance matakin da ya kamata in dauka."

Okonkwo ya ce yana duba yiwuwar hada kai da wasu ‘yan siyasa domin kafa sabuwar tafiya, amma bai kulle kofar sake karfafa jam'iyyar LP ba.

'Kwankwaso, Obi, su hada kai da Atiku' - Surajo Caps

A zantawarmu da wani matashi dan jam'iyyar PDP, Surajo Caps daga jihar Bauchi, ya ce akwai bukatar 'yan adawa su hada kai da Atiku Abubakar domin samun nasara a 2027.

Surajo Caps ya yi ikirarin cewa Atiku ne kawai dan siyasar da zai iya kwace mulki a hannun Shugaba Bola Tinubu a babban zaben kasar na 2027 mai zuwa.

"Duk masu son neman takarar shugaban kasa, da masu son kalubalantar wannan gwamnatin, su kalli kasar, su kalli karfin APC, su kalli halin da talakawa suke ciki.

Kara karanta wannan

An samu rudani kan rasuwar dan wasan Najeriya a kasar waje

"Su tausayawa talakawa fiye da bukatar kansu, su hada hannu karfi da karfe, su taimaki Atiku su mara masa baya, to in sun yi haka, tarihi ba zai manta da su ba.
"Sannan kuma mutanen Arewa, mu kara wayewa, ka da mu yi zaben taliya. Kowa ya yarda cewa zai iya ba da gudunmawa domin kawo sauyi a kasar nan."

- Surajo Caps.

'Atiku, Tinubu, Obi su hakura da takara' - Okonkwo

A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon jigon jam'iyyar LP, Kenneth Okonkwo ya bukaci shugaban ƙasa, Bola Tinubu, Atiku Abubakar da Peter Obi su hakura da takara a 2027.

Okonkwo, wanda ya fice daga LP, ya ce lokaci ya yi da waɗannan manyan ƴan siyasar za su matsa gefe, su ba matasa damar yin shugabanci a ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.