Shehu Sani Ya Taso El Rufai a Gaba, Ya Fadi Asarar da Ya Jawo ga APC

Shehu Sani Ya Taso El Rufai a Gaba, Ya Fadi Asarar da Ya Jawo ga APC

  • Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani ya caccaki tsohon gwamna, Malam Nasir Ahmed El-Rufai
  • Shehu Sani ya bayyana cewa El-Rufai ne silar da ya jawo jam'iyyar APC ta gaza samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa a Kaduna
  • Tsohon sanatan ya kuma nuna ba saboda El-Rufai ba ne mutanen jihar Kaduna suka zaɓi Uba Sani a matsayin gwamna

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Sanata Shehu Sani ya yi magana kan rawar da Nasir El-Rufai ya taka a jihar Kaduna a zaɓen shugaban ƙasa na 2025.

Tsohon sanatan ya ce Nasir El-Rufai ne ke da alhakin rashin nasarar APC a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 a jihar Kaduna.

Shehu Sani ya caccaki Nasir El-Rufai
Shehu Sani ya soki tsohon gwamnan Kaduna, El-Rufai Hoto: @elrufai, @ShehuSani, @ubasanius
Source: Facebook

Shehu Sani ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar Channels tv a shirinsu na 'Hard Copy' a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Shehu Sani: Tsohon sanatan Kaduna ya fadi dalilin komawa jam'iyyar APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar APC ta sha kaye a Kaduna

A zaɓen shugaban ƙasa na 2023, ɗan takarar PDP, Atiku Abubakar, ya lallasa takwaransa na APC, Bola Ahmed Tinubu a jihar Kaduna.

Atiku Abubakar na PDP ya samu ƙuri'u 554,360, inda ya doke Bola Tinubu na APC, wanda ya samu ƙuri'u 399,293.

Peter Obi na jam'iyyar LP ya zo na uku, shi kuma ya samu ƙuri'u 294,494 a zaɓen na shekarar 2023.

Me Shehu Sani ya ce kan El-Rufai?

Shehu Sani ya soki tsohon gwamnan na jihar Kaduna saboda kasa iya sulhunta ɓangarori daban-daban na APC a jihar.

“Daga fahimtata, tsohon gwamnan jihar Kaduna yana cikin fushi da baƙin ciki, wannnan yana daga cikin abin da ke faruwa idan ka yi tsammanin samun wani abu."
“Amma kamar yadda na wallafa a shafina na X, Nasiru ya zama gwamna na tsawon shekaru takwas amma bai iya kawo Kaduna ga Tinubu ba. Sakamakon zaɓen yana nan."

Kara karanta wannan

'Tsufa ke damunka': NNPP ta dura kan Ganduje da ya ce zai raba Abba da kujerarsa

“Idan Nasiru ya ce ya taimakawa Tinubu, bayanan ƙididdiga sun nuna akasin haka. A karo na farko, a zamaninsa, APC ta sha kaye a dukkan kujerun majalisar dattawa guda uku a hannun PDP."
"Daga cikin kujerun majalisar wakilai guda 14, PDP ta samu tara, LP ta samu biyu, APC kuma guda uku kawai."
“Har ila yau yana ikirarin cewa ya kawo Uba Sani kan kujerar gwamna, amma bari mu duba sakamakon, Isa Ashiru na PDP ya samu ƙuri'u 719,000, Uba Sani kuma ya samu 730,000, banbancin ƙuri'u 11,000 ne kawai."
"Kaduna ba ta zaɓi Uba Sani saboda Nasiru ba, a haƙiƙanin gaskiya, Uba Sani ya rasa ƙuri'u saboda shi."
“Wannan mutumin a gefe guda yana yaƙin neman zaɓe ga Uba Sani, a gefe guda kuma yana kunya ta shi."
“Shin yana ganin muhimmancin sulhu? Lokacin da rikicin APC a Kaduna ya ɗauki shekaru bakwai, jam'iyyar ta tura Aminu Masari, Segun Oni, Inuwa Abdulqdir, da John Oyegun don shiga tsakani, amma ya ƙi yarda."
“Kin amincewarsa da yin sulhu da jiga-jigan APC a Kaduna ya haifar da manyan nasarori. Idan da gaske ya amince da yin sulhu, meyasa bai yi a jiharsa ba."

Kara karanta wannan

El Rufa'i ya fadi yadda aikin Ribadu ke taimaka wa 'yan ta'adda da miyagun makamai

- Shehu Sani

A cikin ƴan kwanakin nan, El-Rufai ya zama mai suka sosai ga jam'iyyarsa, yana zargin APC da kaucewa daga manufofinta na asali.

Shehu Sani ya faɗi dalilin komawa APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Shehu Sani ya bayyana dalilin da ya sanya ya koma jam'iyyar APC mai mulki a Kaduna.

Tsohon sanatan na Kaduna ta Tsakiya ya bayyana cewa Gwamna Uba Sani ya taka rawar gani a matakinsa na komawa APC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng