Shehu Sani: Tsohon Sanatan Kaduna Ya Fadi Dalilin Komawa Jam'iyyar APC

Shehu Sani: Tsohon Sanatan Kaduna Ya Fadi Dalilin Komawa Jam'iyyar APC

  • Kwanaki bayan komawarsa jam'iyyar APC mai mulki a jihar Kaduna, Shehu Sani ya fito ya gayawa duniya dalilinsa na yin hakan
  • Tsohon sanatan na Kaduna ya bayyana cewa ko a baya wasu dalilai ne suka sanya ya yi murabus daga jam'iyyar wacce da shi aka kafa ta
  • Kwamred ya bayyana cewa gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya taka rawar gani a matakin da ya ɗauka na komawa APC mai-ci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya yi magana kan dalilinsa na komawa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Shehu Sani ya bayyana cewa tun da farko wasu dalilai ne suka sanya ya yi hijira daga jam'iyyar APC.

Shehu Sani ya yi magana kan komawa APC
Shehu Sani ya fadi dalilin komawa jam'iyyar APC Hoto: Shehu Sani
Asali: Facebook

Tsohon sanatan ya bayyana hakan ne yayin da ake tattaunawa da shi a shirin 'Hard Copy' na tashar Channels tv.

Kara karanta wannan

An yanke makomar Ganduje, APC ta bayyana yankin da ta maida shugabancin jam'iyya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shehu Sani ya yi murabus daga APC a 2018

A watan Oktoban 2018, Shehu Sani, yana wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, ya yi murabus daga APC saboda saɓanin da ya taso dangane da zaɓukan fidda gwani na jam’iyyar.

Daga baya, Shehu Sani ya koma jam’iyyar PDP, ya samu tikitin takarar sanata, amma ya sha kaye a zaɓen 2029, a hannun Uba Sani, wanda a halin yanzu shi ne gwamnan Kaduna.

Meyasa tsohon sanatan ya koma APC?

Da yake magana a shirin na ranar Juma'a, tsohon sanatan ya ce Uba Sani ya ba waɗanda aka ɓatawa rai a baya haƙuri, wanda hakan ya sanya ya yanke shawarar komawa APC.

“Wani yanayi ne ya sa muka fice daga APC a shekarar 2018, amma yanzu wannan yanayin ya sauya, shi ya sa muka koma APC a jihar Kaduna."
“Na farko dai, ina cikin waɗanda aka kafa APC da su musamman a jihar Kaduna. Mun kafa tsare-tsare, mun yi kamfen, kuma mun yi nasara a zaɓen 2015 duka a matakin sanata da gwamna. Amma daga baya muka rabu da gwamnan jihar (Nasir El-Rufai)."

Kara karanta wannan

El Rufa'i ya fadi abin rashin jin dadi da APC ta yi masa da matakin da zai dauka

“Mun rabu ne saboda bambance-bambance da suka haɗa da siyasa, batutuwan ƙashin kai, da kuma al’amuran da suka shafi jihar. Saboda haka, dole muka fice daga jam’iyyar."
“Amma yanzu muna da sabon gwamna wanda ya nemi haɗin kai, ya yi shawarwari tare da gina kyakkyawar alaƙa a faɗin jihar, kuma muka haɗu, muka amince da komawa jam’iyyar da muka kafa a Kaduna.”

- Sanata Shehu Sani

A ranar 16 ga Fabrairu, 2025, Shehu Sani da wasu mambobin jam'iyyun PDP da NNPP sun koma jam’iyyar APC mai mulki a Kaduna.

Shehu Sani ya taɓo batun ƙarin kuɗin data

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bi sahun masu magana kan ƙarin kuɗin data da kamfanonin sadarwa suka yi a Najeriya.

Tsohon sanatan ya bayyana cewa ƴan majalisar tarayya suna da damar da za su iya hana aiwatar da ƙarin kuɗin na kaso 50% da hukumar NCC ta amince da shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng