Ramadan: 'Dan Majalisa Ya Jika Limamai da N40m, Ya Raba Buhunan Abinci 1,000

Ramadan: 'Dan Majalisa Ya Jika Limamai da N40m, Ya Raba Buhunan Abinci 1,000

  • 'Dan Majalisar Tarayya daga jihar Sokoto, Hon. Sani Yakubu ya gwangwaje yan mazabarsa da abubuwan alheri
  • 'Dan siyasar mai wakiltar mazabar Gudu/Tangaza ya ba da tallafin N40m da buhuna 1,000 na shinkafa ga al’umma
  • Hon. Sani Yakubu ya yi wannan abin alheri ne don saukaka wa al'umma yayin azumin watan Ramadan ya gabato
  • Ya tabbatar da karin raba kayan abinci da tufafi kafin Sallah, tare da alkawarin aiwatar da manyan ayyukan raya kasa a yankin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Sokoto - Ana shirin fara azumin watan Ramadan, Hon. Sani Alhaji Yakubu ya ba da tallafin makudan kudi ga yan mazabarsa.

Dan majalisar ya ba da tallafin N40m da buhuna 1,000 na shinkafa ga mutanen yankin Gudu/Tangaza.

Dan Majalisa a Sokoto ya gwangwaje yan mazabarsa saboda azumin Ramadan
Hon. Sani Yakubu ya yi abin alheri ga malamai da al'ummar yankinsa. Hoto: Mubarak Abubakar Balle.
Asali: Facebook

'Dan Majalisa ya rabawa al'umma kaya da kudi

Kara karanta wannan

Ramadan: Tinubu ya tura sako ga Musulmi, ya yi albashir kan farashin abinci da fetur

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimakawa dan Majalisar, Hon. Munzali Lukman ya sanyawa hannu da aka tura wa Legit Hausa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Munzali Lukman ya ce wannan gudunmawa na da nufin tallafa wa iyalai yayin azumi domin samun wadataccen abinci.

Yayin taron, Hon. Sani Yakubu ya tabbatar wa da al’umma cewa za a raba karin kayan abinci da tufafi domin rage musu radadin Ramadan da Sallah.

Haka nan, ya sake jaddada kudirinsa na aiwatar da ayyuka kamar: mayar da wutar lantarki daga Kware zuwa Tangaza da Gudu, da gina hanyoyin Sakkwai-Gongono da Tangaza-Baidi.

Sauran ayyukan sun hada da gina gadar da za ta hada Takkau da Wayage, da wata gadar da za ta hada Gwazange da Bachaka domin saukaka zirga-zirga.

Dan Majalisar Tarayya a Sokoto ya ba malamai kudi da buhunan abinci 1,000 ga al'umma

Yadda dan Majalisa a Sokoto ya kyautatawa limamai

Sanarwar ta ce:

"An ba da N4m ga masu amfani da kafafen sada zumunta daga mazabar, N2m ga 'yan kungiyar NURTW na Gudu da Tangaza, da N1m ga masu babura."

Kara karanta wannan

Bayan duba wata, Sarkin Musulmi ya fadi ranar fara azumin Ramadan a Najeriya

Wani daga cikin yaran dan Majalisar, Mubarak Abubakar Balle ya tattabar da haka ga wakilin Legit Hausa a yau Juma'a 28 ga watan Faburairun 2025.

Balle ya ce dan Majalisar ya ba dukan limaman Juma'a a yankinsa N100,000 domin sararawa a azumin watan Ramadan.

Ya ce:

"Wannan shi kuma kwana uku da suka gabata ne Hon. Sani Yakubu ya rabawa gaba daya limaman Juma'a na yankinsa N100,000 domin su fara shirin shiga azumin watan Ramadan."

Balle ya kuma fadi abubuwan alheri da dan Majalisar ke yi da suka hada da gyaran wutar lantarki a wasu kananan hukumomi biyu da suka shafe tsawon shekaru 10 babu ita.

Wadannan shirye-shirye na nuni da jajircewar Hon. Sani Yakubu wajen inganta jin dadi da ci gaban al’ummarsa.

Gwamna Aliyu ya gwagwanje malaman Musulunci

Kun ji cewa Gwamna Ahmed Aliyu ya yi abin alheri ga malaman Musulunci yayin da ake shirin fara azumin Ramadan.

Kara karanta wannan

Ramadan: Ɗan majalisa a Arewa ya tara talakawa, ya raba masu kudi da kayan abinci

Gwamnan ya ware buhunan masara da kuɗafe domin rabawa limamai, na'ibai, malamai da kungiyoyi albarkacin Ramadan a Sokoto.

Gwamna Aliyu ya ce za a ba wasu manyan malamai 300 kowane N200,000 da ƙarin wasu malamai 100 da za a bai wa kowanensu N100,000 domin shiga azumin Ramadan da nauyinsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.