‘Tsufa ke Damunka’: NNPP Ta Dura kan Ganduje da Ya Ce Zai Raba Abba da Kujerarsa
- Shugaban jam'iyyar NNPP a jihar Osun, Tosin Odeyemi, ya caccaki Abdullahi Ganduje kan shirin APC na karɓe Kano, yana mai cewa babu yiyuwar hakan
- Odeyemi ya ce shugaban APC bai san halin da talakawan Kano ke ciki ba, kuma suna goyon bayan Gwamna Abba Yusuf da ke aiki tukuru
- Ya kalubalanci Ganduje da ya shirya gangami a kan tituna a Kano don ganin ko masu goyon bayansa za su bayyana
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Osun - Shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Osun, Tosin Odeyemi ya dura kan shugababn APC, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
Odeyemi ya caccaki Ganduje kan shirin jam’iyyarsa na kwace Kano a zaɓen gwamna mai zuwa a shekarar 2027.

Asali: Facebook
NNPP a Osun ta gargadi Ganduje kan kalamansa
A martaninsa kan furucin Ganduje cewa NNPP jam’iyya ce na shirin mutuwa, Odeyemi ya bukace shi ya farka daga mafarkin da yake yi, cewar The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Odeyemi ya wannan buri ne maras tushe, inda ya ce hakan na nuna Ganduje bai san halin da talakawa ke ciki ba, domin suna tare da Gwamna Abba Yusuf.
Ya ce irin ayyukan da Abba Kabir Yusuf ke yi a Kano ya wuce a yi masa barazana da zabe saboda al'ummar jihar suna matukar kaunarsa kowa ya sani a zahiri.
'Abin dariya ne Ganduje ya ce zai kwace Kano' - NNPP
A cikin wata sanarwa, ya ce:
“Abin da ke faruwa a Kano ya fi ƙarfin abin da tsohon gwamna zai iya yi wa raga-raga."
"Na yi dariya da jin wannan furuci, kodayake Baba Ganduje ya tsufa, ba zan zarge shi sosai ba, amma ya sani Kano ta canza."
"Ina ga mutum da ke nesa da jiharsa zai yi alfahari cewa manyan NNPP za su koma APC saboda ya raba motoci da babura?"
"Talakawan Kano suna tare da Gwamna Abba Yusuf, wanda ke yin iya ƙoƙarinsa don inganta rayuwarsu ta kowane ɓangare."

Asali: Twitter
An kalubalanci Ganduje kan siyasar jihar Kano
Odeyemi ya kalubalanci Ganduje ya gwada hada gangami a Kano ya gani ko al'umma za su tururuwa.
Ya kara da cewa:
"Ya kamata Ganduje ya shirya gangami a titi a Kano don ganin ko wani zai mara masa baya. Mun nuna musu yadda ake yi wa jama'a hidima."
"Shugaban APC ya daina dogaro da rahotannin ƙarya daga masu ba shi shawara, waɗanda ke yaudararsa cewa jam’iyyarsa za ta kwace Kano."
Saukin abinci: Ganduje ya yabawa kokarin Tinubu
Kun ji cewa Shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya yabawa tsare-tsaren tattalin arzikin Bola Tinubu da cewa suna haifar da ci gaba da rage tsadar kayayyaki a kasar.
Ganduje ya bayyana haka ne a yayin wani shirin tallafi da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I Jibri, ya shirya a jihar Kano.

Kara karanta wannan
A gaban Tinubu da manyan jiga jigai, Ganduje ya bankado abubuwan da ya tarar a APC
Tsohon gwamnan Kano, ya bukaci al’ummar jihar Kano su goyi bayan gwamnatin Tinubu domin tabbatar da ci gaba a fadin kasar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng