'Zabinka ne': APC Ta Ƙaryata El Rufai, Ta Zargi Abin da Ya Hana Shi Halartar Taro a Abuja
- Jam’iyyar APC ta yi martani kan maganar Nasir El-Rufai game da rashin halartar taron jam'iyyar APC da aka yi a birnin Abuja
- Jam'iyyar ta ce an aika wa Nasir El-Rufai da sanarwar taron NEC, amma rashin halartarsa zabi ne nasa, ba don wai bai samu gayyata ba
- El-Rufai a bangarensa, ya ce bai samu gayyata da wuri ba kafin taron, ya kuma bayyana cewa yana da shirin tafiya Cairo don yin ayyukansa na Ramadan
- Kakakin APC, Felix Morka, ya ce sauran manyan jam’iyyar sun samu irin sanarwar da aka aika wa El-Rufai, kuma sun halarta ba tare da matsala ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Jam’iyyar APC ta mayar da martani kan rashin halartar Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan Kaduna, a taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) da aka gudanar.

Kara karanta wannan
El-Rufai ya kawar da jita jita, ya fadi dalilin rashin halartar taron APC a Abuja
Jam'iyyar ta soki El-Rufai bayan kalamansa da yake cewa rashin samun gayyata da wuri shi ne dalili.

Source: Facebook
Dalilin El-Rufai na kin halartar taron APC
A hira da Channels TV, kakakin APC, Felix Morka, ya ce rashin halartar El-Rufai shi ne zabinsa, ba wai bai samu gayyata ba.
A ranar Laraba, mambobin jam’iyyar mai mulki sun hallara a sakatariyarta da ke Abuja don taron NEC na farko tun Agusta 2023.
Kwamitin NEC shi ne mafi girman rukunin yanke hukunci a APC, wanda ya kunshi gwamnoni, tsofaffin shugabanni, da shugabannin majalisun dokoki.
Sai dai, El-Rufai wanda ke sukar jam’iyyarsa bai halarta ba, haka nan, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da Rotimi Amaechi suma ba su halarta ba.
A wata hira da Arise TV ranar Litinin, El-Rufai ya ce bai samu isasshen sanarwa ba, kuma yana da wasu shirye-shirye na tafiya zuwa Cairo.

Source: Facebook
Taron NEC: APC ta soki El-Rufai kan kalamansa
Sai dai Morka ya ce El-Rufai ya samu irin sanarwar da sauran manyan jam’iyyar suka samu, amma ya zabi ka da ya zo.

Kara karanta wannan
Tsohon shugaba Buhari, El-Rufa'i da sauran jagororin APC sun ki halartar taron APC
Morka ya ce:
"An kira sunayen manyan mambobi da suka halarci taron, El-Rufai ya samu irin sanarwar da suka samu, amma bai zo ba.
"Da yana son zuwa, tabbas zai halarta, wasu da ba su Abuja sun yi shiri suka taho domin wannan taro.
"Ba zan ce komai ba, amma ba ni da tabbacin ko El-Rufai mamba ne na NEC, a matsayinsa, yana cikin kwamitin caucus.
Tinubu ya fadi abin da ke damun El-Rufai
A baya, mun ba ku labarin cewa Hadimin Bola Tinubu a bangaren sadarwa, Bayo Onanuga ya yi martani kan kalaman Malam Nasir El-Rufai.
Onanuga ya ce El-Rufai na jin haushi ne saboda ba a ba shi minista ba, duk da kokarinsa wajen tabbatar da Tinubu ya zama shugaban kasa.
Hadimin ya bukaci El-Rufai da ya daina guna-guni, ya ce Tinubu ya san irin kokarinsa, amma ba lallai ne a ce sai an ba shi mukami ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng