'Yadda Buhari Ya Dara Obasanjo, Yar'Adua da Goodluck Jonathan a Lokacin Mulkinsa'

'Yadda Buhari Ya Dara Obasanjo, Yar'Adua da Goodluck Jonathan a Lokacin Mulkinsa'

  • Tsohon hadimin Muhammadu Buhari ya magantu kan salon mulkin dattijon daga shekarar 2015 zuwa 2023
  • Bashir Ahmad, ya ce gina abubuwan more rayuwa a lokacin mulkinsu ya zarce na mulkin Obasanjo, Jonathan da Yar'Adua
  • Matashin ya rubuta hakan ne a shafin X, yake cewa wadannan shugabanni uku ba su yi abin da Buhari ya yi ba
  • Wannan na zuwa ne bayan rubutu da wani shafin PDP ya yi cewa a mulkin Obasanjo zuwa Jonathan, an shakata

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Tsohon hadimin Muhammadu Buhari ya ce aikin da mai gidansa ya yi ya fi na lokacin tsofaffin shugabannin uku.

Bashir Ahmad ya fadi hakan ne yayin mayar da martani ga PDP game da salon mulkin Olusegun Obasanjo da Umaru Musa Yar'adua da Goodluck Jonathan.

Kara karanta wannan

A gaban Tinubu da manyan jiga jigai, Ganduje ya bankado abubuwan da ya tarar a APC

Hadimin Buhari ya fadi inda mai gidansa ya dara Obasanjo, Yar'Adua da Jonathan a mulki
Bashir Ahmad ya ce Buhari ya fi Obasanjo, Yar'Adua da Jonathan a ci gaban gine-gine a Najeriya. Hoto: Muhammadu Buhari, Goodluck Jonathan.
Asali: Facebook

Bashir Ahmad ya fadi ƙoƙarin Buhari a mulki

Bashir Ahmad ya bayyana haka ne a shafinsa na X a yau Laraba 26 ga watan Fabrairun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon hadimin Buhari ya bayyana cewa ci gaban gine-ginen gwamnatin Buhari ya fi na zamanin Obasanjo, Jonathan da marigayi Yar'Adua.

A cikin rubutun, Bashir Ahmad ya ce:

"Abin dariya ne! Idan ana maganar ci gaban gine-gine, wadannan shugabanni uku tare ba za su iya yin ikirarin koda daya bisa uku na abin da Shugaba Buhari ya cimma a cikin shekaru 8 ba.
"Wannan ba ra'ayi ba ne, gaskiya ce."

Wannan ikirari na Bashir Ahmad ya nuna manyan ayyuka da gwamnatin Buhari ta zuba a fannoni kamar su sufuri, makamashi da noma.

Yan Najeriya da dama sun yi martani kan rubutun Bashir Ahmad inda wasu da yawa suka caccake shi.

Duk da haka an samu mabambantan ra'ayi inda wasu yan ƙalilan suka yi yabo a bangaren ci gaba da kuma manyan ayyuka.

Kara karanta wannan

Littafin IBB: Fitaccen Lauya, Falana zai maka Janar Babangida a kotu, ya jero dalilai

Martanin wasu yan Najeriya kan lamarin

@davidoghe:

"Na ji dadin yadda ka zama mai biyayya ga mai gidanka, nima haka zan yi."

@Anitlaurel:

"Buhari shi ne mafi munin shugaban kasa a Najeriya da ba ta taɓa yi ba, Tinubu yana kokari sosai wurin ganin ya karya tarihin!!! Shirme"

@Stazinga:

"Kan gadar '2nd Niger Bridge' zan iya cewa Buhari yana da abin fada a bangaren manyan ayyuka."

@Baturekovsky:

"Ahmad, tambaya daya kawai, za ka iya fadamin dalilin da ya sa Buhari bai kawo ci gaba ba a aikin Mambila?"

@EnejereMichael:

"Obasanjo ne ya kawo abin da ake amfani da shi (wayar salula) wurin fadin ra'ayinka, ka fadamin abu daya da Buhari ya kawo da ya taimaki yan Najeriya, abu daya kawai."

Dalilin rashin ganin Buhari a taron APC

Mun ba ku labarin cewa tsohon shugaban ƙasan Najeriya, Muhammadu Buhari bai samu damar halartar babban taron jam'iyyar APC da aka yi a Abuja ba.

Kara karanta wannan

Tinubu zai sauke Ganduje a shugaban APC? Sakataren jam'iyya ya magantu

Hakazalika manyan ƙusoshin APC da suka haɗa da Nasir El-Rufai, Rotimi Amaechi da Kayode Fayemi ba su samu zuwa taron ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.