Barau Jibrin Ya Kara Ragargazar Abba, Mawakin Kwankwasiyya Ya Koma APC
- Fitaccen mawakin Kannywood, Abubakar Sani Dan Hausa ya bar NNPP da Kwankwasiyya, ya koma APC
- Rahotanni sun nuna cewa mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin ne ya tarbi mawakin a Abuja
- Jama’a sun bayyana ra’ayoyinsu kan sauyin shekar mawakin, wasu na masa fatan alheri wasu kuma akasin haka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya karɓi fitaccen mawakin Kannywood, Abubakar Sani Dan Hausa da ya sauya sheka daga NNPP zuwa APC.
Dan Hausa da aka san shi da goyon bayan tafiyar Kwankwasiyya a baya, ya bayyana cewa ya yanke shawarar mara wa APC baya domin bayar da gudunmawarsa wajen ci gaban Najeriya.

Asali: Facebook
Sanata Barau Jibrin ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X, yana mai maraba da mawakin zuwa jam’iyyar APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Barau Jibrin ya karɓi Dan Hausa
A yayin tarbar Abubakar Sani Dan Hausa a gidansa da ke Abuja, Sanata Barau Jibrin ya jaddada cewa APC za ta ci gaba da hada kai da mutane masu kishin kasa domin gina Najeriya.
"Na karɓi Abubakar Sani Dan Hausa, mawaki mai fasaha daga masana’antar Kannywood, wanda a baya yana cikin NNPP da tafiyar Kwankwasiyya.
"Yanzu ya yanke shawarar komawa jam’iyyarmu ta APC,"
Ya kuma tabbatar da cewa za su yi aiki tare domin inganta rayuwar al’umma da kawo ci gaba ga kasa.

Asali: Facebook
Ra’ayoyin jama’a kan matakin Dan Hausa
Bayan bayyanar wannan labari, mutane da dama sun bayyana ra’ayoyinsu kan sauyin shekar mawakin zuwa APC.
Wasu jama'a sun taya shi murna, yayin da wasu suka bayyana shakku game da wannan matakin da ya dauka.
Abubakar Iliyasu ya ce:
"Ina taya shi murna, Allah ya albarkace shi ya kuma yi masa jagora. Ina yi masa fatan alheri."
Mamman Hausawa ya nuna shakku game da sauyin shekar Dan Hausa, inda ya ce:
"Wallahi wankarka suke yi. Idan kana so ka tabbatar, ka gwada daina ba su kudi, sai ka gani idan za ka sake samun wani da sunan ya dawo tafiyarka. Shawara kyauta."
Prince Rabi'u Aminu ya bayyana cewa sauyin shekar mawakin ba zai yi tasiri ba a siyasa, inda ya ce:
"Dan Hausa ba zai kawo maka kuri’u daga mazabarsa ba, DSP. Sai dai ka ci gaba da tallafa wa matasa ta hanyar ilimi, hakan ne zai ba ka nasara a Kano in sha Allah."
Shin Dan Hausa zai tsaya a APC?
Wasu daga cikin masu sharhi sun yi zargin cewa Dan Hausa na iya komawa tafiyar Kwankwasiyya nan gaba.
Hamza Hassan Planner ya ce:
"Kana kokari amma Wallahi sai ya koma Kwankwasiyya. Ya kamata ka maida hankalinka wajen kyautata wa ‘yan jam’iyya, ka rabu da ‘yan wankiyan nan."

Kara karanta wannan
Barau ya rikita Kano da kyautar motoci da babura, ya yi alkawari ga matasa da malamai
A gefe guda, Abubakar Yusuf Funtua ya bukaci Sanata Barau da ya ba Dan Hausa cikakken goyon baya:
"Maganar gaskiya, Abubakar Sani tabbas dan Kwankwasiyya ne na asali kuma mutum ne mai akida sosai. Ina fatan za ka riƙe shi da amana kuma ka taimaka masa yadda ya dace."
APC ta yi magana kan makomar Ganduje
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki ta yi magana kan rade radin sauke shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje.
Sakataren jam'iyyar ya ce labarin sauke Ganduje ba shi da asali kuma zai cigaba da jagorantar APC kamar yadda ya fara a baya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng