Tsohon Shugaba Buhari, El Rufa'i da Sauran Jagororin APC Sun Ki Halartar Taron APC

Tsohon Shugaba Buhari, El Rufa'i da Sauran Jagororin APC Sun Ki Halartar Taron APC

  • Shugabannin APC na kasa, ciki har da Bola Ahmed Tinubu sun halarci babban taron jam'iyyar dake gudana a babbar sakatariyarsu a Abuja
  • Sai dai ba a ga wasu kusoshin APC kamar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i a taron ba
  • Kafin nan Buhari ya gujewa taron kaddamar da littafin tarihin Ibrahim Babangida, shi kuwa Nasir El-Rufai ya ce zai bar Najeriya kafin zaman

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Shugabannin APC sun tattaru a babbar sakatariyar jam'iyyar dake Abuja domin gudanar da taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC).

An rufe dukkan hanyoyin da ke kai wa wajen taron yayin da jami’an tsaro masu dauke da makamai, ciki har da sojoji suke kai koma a titunan.

Kara karanta wannan

"Tsintsiya madaurinki daya mu ke," Gwamnan APC ya yi watsi da zargin El-Rufa'i

Buhari
Shugabannin APC sun yi watsi da taron jam'iyya Hoto: Nasir El-Rufa'i/Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Channels TV ta ruwaito cewa, duk da cewa jam’iyyar ta fitar da jerin sunayen 'yan jaridu da aka amince da su shiga taron a safiyar Laraba, an hana da yawansu shiga harabar taron.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadanda aka hango a taron jam'iyyar APC

Gwamnoni daga jihohin Edo, Benue, Ondo, Ekiti, Kaduna, Jigawa, Nasarawa, Yobe, Niger, Lagos, Kogi, Ogun, da Imo sun halarci taron.

Haka kuma, an hango mataimakin gwamnan Ebonyi da tsofaffin gwamnonin jihohin Kogi, Kebbi, Niger, Zamfara, da Plateau a wajen taron.

Daga cikin wadanda suka iso da wuri sun hada da tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari; Ministan Tsare-tsaren Ƙasa da Kasafin Kuɗi, Atiku Bagudu.

Wadanda ba su halarci taron APC NEC ba

Yayin da APC ke babban taronta na kasa, wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyyar sun gaza halartar taron, ciki har da tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Muhammadu
Tsohon shugaban kasa bai halarci taron NEC na APC ba Hoto: Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Sauran wadanda ba a gani a wajen taron ba sun hada da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai

Kara karanta wannan

Shirin babban taron APC ya gama kankama, jagororin jam'iyya sun hallara Abuja

Haka zalika babu duriyar tsohon mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi da Kayode Fayemi.

Zuwa yanzu, babu wasu bayanai da ke karin haske a kan abin da ya hana manyan jam'iyyar halartar taron da aka sa ran manyan za su halarta.

Shugaba Tinubu ya halarci taron APC

Jagoran jam’iyyar APC, shugaba Bola Tinubu, Mataimakinsa, Kashim Shettima, da Shugaban Majalisar Dattawa, Goodwill Akpabio, sun isa sakatariyar APC da rana.

Su na tare da Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, kuma shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ne ya jagoranci gudanar da taron.

An tsaurara tsaro a taron APC

A baya, mun wallafa cewa an samar da wadataccen tsaro a babban taron APC da ya gudana a babban birnin tarayya Abuja, wanda ya zama karon farko na irin wannan zama a 'yan kwanakin nan.

Ana sa ran taron zai yi duba a kan muhimman batutuwan da ke damunta, musamman ganin yadda zaman ya zo a lokacin da wasu manyan jam'iyyar ke kuka ga tsarin gudanarwarta.

Kara karanta wannan

Tinubu zai sauke Ganduje a shugaban APC? Sakataren jam'iyya ya magantu

Haka kuma taron ya zo a gabar da wasu ke tsammanin APC ta na kokarin sauke shugabanta na kasa, Abdullahi Umar Ganduje.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.