"Ku Canza Tunani," Akume Ya ba Atiku, El Rufai da Gwamna Bala Shawara kan Takara a 2027
- Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ya bukaci Atiku Abubakar da sauran ƴan siyasar Arewa su mutunta tsarin karɓa-karɓa a 2027
- Sanata Akume ya ce bai kamata manyan ƴan siyasar Arewa su nemi karɓar mulki a 2027 ba saboda Bola Tinubu da yankin kudu ba su cinye wa'adinsu ba
- Ya ce tun da tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya yi shekaru takwas, ya kamata a bar Kudu ta yi shekaru takwas kafin mulki ya dawo Arewa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bauchi - Yayin da Najeriya ke kara kusantar zaben 2027, sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Sanata George Akume, ya bukaci manyan ƴan siyasar Arewa su haƙura da takara a 2027.
Sanata Akume ya buƙaci tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, Gwanna Bala Mohammed, Nasir El-Rufai da sauransu su mutunta tsarin karɓa-karɓa.

Asali: Facebook
Sakataren gwamnatin ya ce mutunta tsarin karɓa-karɓa tsakanin Arewa da Kudu zai ƙara danƙon haɗin kan ƙasa, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akume ya bayyana hakan ne a Bauchi yayin taron tunawa da marigayi Sir Ahmadu Bello Sardauna wanda aka shirya karo na 11 tare da bayar da lambobin yabo ga wasu fitattun ‘yan siyasa da shugabanni.
Akume ya buƙaci a mutunta tsarin karɓa-karɓa
Akume wanda Christopher Tarkaa ya wakilta, ya jaddada cewa mutunta tsarin karɓa-karɓa a mulkin Najeriya zai taimaka wajen tabbatar da adalci, daidaito, da kuma ci gaban dimokuradiyya.
Ana rade-radin cewa wasu manyan shugabannin Arewa, musamman Atiku, Malam Nasir El-Rufai, da Bala Mohammed, na shirin tsayawa takarar shugaban kasa a 2027.
Wasu na ganin hakan na iya kawo matsala a siyasar kasar, duba da cewa yankin Kudu na iya bukatar shekaru takwas a mulki kafin mulki ya dawo Arewa a 2031.
Wannan na zuwa ne bayan tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya yi shekaru takwas a mulki daga 2015 zuwa 2023, kafin mulki ya koma Kudu a 2023.
Sanata Akume ya ce tsarin karɓa-karɓar mulki yana da matukar muhimmanci wajen daidaita siyasar Najeriya, rahoton Punch.

Asali: Facebook
2027: An roki ƴan Arewa su zaɓi Tinubu
Ya bukaci shugabanni da ƴan siyasar Arewa da su mutunta tsarin da aka dade ana amfani da shi domin kare hadin kai da kuma tabbatar da adalci ga kowane yanki.
“Ina rokon ‘yan Arewa da su goyi bayan Shugaba Bola Tinubu domin dorewar hadin kai da ci gaban Najeriya. Shugaban kasa yana da kyakkyawan niyya ga kasar nan.”
"Wajibi ne mu fifita hadin kan kasa fiye da son zuciyarmu," in ji Akume.
Ya kuma ja hankalin shugabannin siyasa da su kaucewa yunkurin da ka iya jefa Najeriya cikin rudani kamar yadda aka gani a kasashen Somaliya, Libya, da Iraki.

Kara karanta wannan
APC ta yi bayani kan ƴan Majalisa 27 da ake zargin sun sauya sheka daga PDP zuwa cikinta
El-Rufai ya fara juyawa Tinubu baya
A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ce yana son wani ɗan Kudu ya maye gurbin Bola Tinubu a 2027.
El-Rufai ya nuna cewa gara a samu wani ɗan Kudu ya karɓi mulkin Najeriya a 2027 ma'ana dai kada shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya yi tazarce.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng