NEC: Bayan Ganawa da Tinubu, An Ji Muhimman Abubuwan da Za a Tattauna a Taron APC
- Shugabanni da jiga-jigan jam’iyyar APC sun hallara a Abuja domin taron NEC, wanda shi ne na farko tun bayan watan Satumba 2023
- Shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje ne zai jagoranci taron, wanda zai maida hankali kan hadin kai da sulhunta ‘ya’yan jam’iyyar
- Ana sa ran shugaba Bola Tinubu zai yi jawabi kan shirin ‘Renewed Hope Agenda’, tare da tattauna shirin zabuka da shari’o’in jam’iyyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugabanni da kusoshin jam’iyyar APC sun hallara a birnin Abuja domin gudanar da muhimman tarukan jam’iyyar.
A yau, 26 ga Fabrairu, 2025, za a gudanar da taron kwamitin zartaswa na kasa (NEC), wanda shi ne na farko tun bayan watan Satumbar 2023.

Asali: Twitter
APC za ta gudanar da taron NEC yau
Kwamitin NEC shi ne mafi girman kwamitin yanke hukunci a jam’iyya, wanda ke da ikon juya jam'iyyar gabanin gudanar da babban taronta, inji rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamitin dattawan jam’iyyar na da hakkin ba da shawara, kuma yana gabatar da shirin da za a tattauna a taron NEC.
Shugaban jam’iyyar na kasa, Dr. Abdullahi Ganduje, ne zai jagoranci taron NEC a wannan karon.
Taron na zuwa ne bayan wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar, kamar tsofaffin gwamnonin Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da Ekiti, Dr. Kayode Fayemi, sun koka kan dadewar da aka yi ba tare da kiran taron ba.
Haka nan, sun bayyana wasu korafe-korafe dangane da salon mulkin Shugaba Tinubu da yadda jam'iyyar ke tafiyar da lamuranta.
Abubuwan da za a tattauna a taron APC-NEC
Taron NEC ya kunshi mambobin kwamitin dattawa, kwamitin aiki na kasa (NWC), da shugabannin jam’iyya na jihohi.

Kara karanta wannan
Bayan kalaman El Rufai, Tinubu, Shettima, Ganduje sun kira taron kusoshin APC a Abuja
Wata majiya ta ce an kira wannan taron ne domin nazarin ci gaban jam’iyyar a cikin kusan shekaru biyu da suka wuce.
A cewar majiyar:
“APC na cika wajibcin kundin tsarin mulkinta na gudanar da taron NEC. Manufar taron ita ce duba ci gaban da aka samu a kokarin karfafa jam’iyyar a matsayin mai mulki.
“Daga cikin batutuwan da za a tattauna har da kokarin tabbatar da hadin kai da zaman lafiya a jam’iyya. Za a kuma duba ci gaban da aka samu a kokarin sulhunta ‘ya’yan jam’iyyar a wasu jihohi.
“Za a tattauna batun shigar da sababbin mambobi, musamman wadanda suka sauya sheka daga wasu jam’iyyu.''
Tinubu zai yi jawabi a taron APC NEC

Asali: Twitter
Majiyar ta kara da cewa:
"Sai kuma batun zabukan da ke tafe, ciki har da na gwamna a jihar Anambra a watan Nuwamba, da kuma shirin zabukan gwamna a jihohin Ekiti da Osun a shekara mai zuwa.”
Taron NEC zai kuma saurari rahoton shari’o’in da ke shafar jam’iyya a matakin kasa da jihohi, da ayyukan kwamitocin jam’iyya da cibiyar Progressive Institute.
Majiyar ta kara da cewa, ana sa ran Shugaba Tinubu zai yi bayani kan wasu muhimman manufofin gwamnati da suka shafi cika alkawurran da ke cikin shirin ‘Renewed Hope Agenda’ na gwamnatinsa.
Tinubu ya jagoranci taron kusoshin APC
A daren jiya, muka ruwaito cewa, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci taron kwamitin kusoshin jam’iyyar APC a dakin taro na fadar shugaban kasa, Aso Villa.
Shugabanni daga yankunan kasar sun halarta, ciki har da gwamnoni, ministoci, tsofaffin gwamnonin APC, da shugabannin majalisa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng