Muƙamin Minista: Tinubu Ya Fadi Abin da ke Damun El Rufai, Ya ba Shi Shawarwari
- Hadimin Bola Tinubu a bangaren sadarwa, Bayo Onanuga ya yi martani kan kalaman Malam Nasir El-Rufai a hira da yan jarida
- Onanuga ya ce El-Rufai yana jin haushi saboda ba a ba shi minista ba, duk da kokarinsa wajen tabbatar da Tinubu ya zama shugaban kasa
- Hadimin ya bukaci El-Rufai da ya daina guna-guni, ya ce Tinubu ya san irin kokarinsa, amma ba lallai ne a ce sai an ba shi mukami ba
- A wata hira, El-Rufai ya ce ba Majalisa ce ta hana shi zama minista ba, sai dai Shugaban kasa Tinubu da kansa ya ki ba shi mukami
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Hadimin Shugaba Bola Tinubu kan harkokin sadarwa, Bayo Onanuga ya mayar da martani ga Nasir El-Rufai.
Onanuga ya ce tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, yana jin haushi ne saboda ba a ba shi mukamin minista ba.

Asali: Twitter
Minista: Tinubu ya ba El-Rufai shawara
Onanuga ya fadi haka ne a shirin Sunrise Daily na Channels TV a yau Talata 25 ga watan Fabrairun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nasir El-Rufai na daga cikin wadanda aka shirya nada shi minista, amma daga bisani Majalisar Dattawa ta cire sunansa daga jerin wadanda aka tantance.
Bayan wannan al’amari, El-Rufai ya fara sukar gwamnati da jam’iyyar APC, yana cewa an fi bai wa na kusa da Tinubu da yan Kudu mukami.
A wata hira, El-Rufai ya ce ba Majalisar Dattawa ba ce ta hana shi zama minista, amma Tinubu da kansa ya yanke shawarar kin ba shi mukami.

Tinubu ya ce yana sane da kokarin El-Rufai
A cikin shirin, Onanuga ya ce duk da irin kokarin da El-Rufai ya yi, lokaci ya yi da zai manta da batun.
A ɓangarensa, Onanuga ya ce:
"Ina jin tausayinsa, yana jin haushi, amma lokaci ya yi da zai ci gaba da rayuwarsa.
"Ba zai yiwu mutum ya ci gaba da kuka kamar wani yaro da aka kwace wa abinci ba, ya kamata ya wuce.
"A dabi’a, zai iya jin haushi, amma Shugaban kasa ya riga ya yaba da irin rawar da El-Rufai ya taka wajen nasarar zabensa."
Onanuga ya ce yana da kyau a fahimta cewa Tinubu bai manta da kokarin El-Rufai ba, amma rashin mukami ba yana nufin an kore shi gaba daya ba.
Ya bukaci El-Rufai da ya hakura, ya ce tun daga 1999 yana kan mukamai, don haka lokaci ya yi da zai ci gaba da rayuwarsa ba tare da damuwa ba.
Ribadu ya yi martani ga kalaman El-Rufai
Mun ba ku labarin cewa mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Mallam Nuhu Ribadu ya yi martani game da kalaman tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.
Ribadu ya ce ba zai yi ta gardama da Nasir El-Rufai ba, ya ce yana da abubuwan da suka fi muhimmanci a ayyukansa fiye da jayayya da shi ka lamarin.

Kara karanta wannan
'Don Allah ka bar ni': Ribadu ya yi martani ga El-Rufai bayan kalamansa kan zaben 2031
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng