El Rufa'i Ya Fadi Abin Rashin Jin Dadi da APC Ta Yi Masa da Matakin da zai Dauka

El Rufa'i Ya Fadi Abin Rashin Jin Dadi da APC Ta Yi Masa da Matakin da zai Dauka

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce jam’iyyar APC da ya taimaka aka kafa ta, ta yi watsi da shi a yanzu
  • Ya bayyana cewa ba zai koma jam’iyyar PDP ba, domin hakan kamar sauka daga wani layi mai sarkakiya ne zuwa mafi muni
  • Nasir El-Rufai ya ce yana fatan jam'iyyar APC za ta dawo kan turbar da ta dace domin ya ci gaba da kasancewa a cikinta

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, ya bayyana rashin jin dadinsa game da tafiyar da jam’iyyar APC, wacce ya ce ta yi watsi da shi.

El-Rufai, wanda ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi a karon farko bayan sauka daga gwamna, inda ya ce ba zai koma jam’iyyar PDP ba duk da matsalolinsa da APC.

Kara karanta wannan

2027: El Rufa'i ya fadi kalubalen da za a fuskanta wajen tallar Tinubu a Arewa

El-Rufa'i
El-Rufa'i ya ce da APC ya ke da matsala ba Bola Tinubu ba. Hoto: Bayo Onanuga|Nasir El-Rufa'i
Asali: Facebook

A hirar da ya yi da Arise TV, tsohon gwamnan ya ce matsalarsa ba da shugaba Bola Tinubu ba ba ce, illa dai da yadda jam’iyyar ke tafiyar da al’amuranta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

El-Rufai ya koka kan halin da APC ke ciki

Tsohon gwamnan ya bayyana damuwarsa kan yadda jam’iyyar APC ke tafiyar da al’amuranta, yana mai cewa ba ta cika alkawuran ci gaban da ta dauka ba.

El-Rufa'i ya ce:

“Ni daya ne daga cikin wadanda suka kafa APC, kuma har yanzu ina cikinta. Amma ina da damuwa kan yadda ake tafiyar da ita.
"Shekaru biyu kenan, amma jam’iyyar ba ta gudanar da tarukan da ya kamata ba.”

Ya kara da cewa:

"Ba a tattauna dangantakar gwamnati da manufofin jam’iyyar ba. Sai yanzu na ji a ɓoye cewa za a yi taron kwamitin gudanarwa na kasa da na NEC.”

El-Rufai ya ce ba zai koma PDP ba

Kara karanta wannan

El Rufa'i ya fadi matsayarsa a kan sake neman takara a Najeriya

El-Rufai ya ce duk da matsalolinsa da APC, ba zai taba komawa PDP ba domin hakan tamkar fita ne daga matsala zuwa wata mafi muni.

Atiku
El-Rufa'i da babban jigo a PDP a wajen taro. Hoto: Nasir El-Rufa'i|Atiku Abubakar
Asali: Twitter

Tsohon gwamnan ya ce:

“A yanzu ban san matakin da zan dauka ba idan APC ba ta dawo kan turbar da ta dace ba, amma abu daya da na tabbata da shi, shi ne ba zan koma PDP ba.”

Tsohon gwamnan ya ce PDP ta kara tabarbarewa fiye da yadda take a da, don haka ba ita ce madogara ba.

'Ba dole ba ne a ba ni mukami' – El-Rufai

El-Rufai ya bayyana cewa ba lallai ba ne a ba shi mukami a gwamnatin APC duk da irin gudunmawar da ya bayar wajen kafa ta.

A karshe, ya ce yana nan daram a siyasa, kuma idan APC ba ta gyara ba, zai iya samun wata hanyar da zai ci gaba da fafutukar manufofin da ya ke yi imani da su.

Kara karanta wannan

'Ku tambaye shi, ya sani': El-Rufai ya fadi yadda Buhari ya tilasta masa neman gwamna

Jam'iyyar PDP ta ce za ta karbi El-Rufa'i

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta ce kofar ta a bude take domin karbar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i.

Hakan na zuwa ne yayin da tsohon gwamnan ke maganganu da suke nuna cewa akwai matsala tsakaninsa da jam'iyyarsa ta APC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng