'Ku Tambaye Shi, Ya Sani': El Rufai Ya Fadi Yadda Buhari Ya Tilasta Masa Neman Gwamna
- Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi magana kan wanda ya tilasta masa neman takarar gwamna
- El-Rufai ya ce Muhammadu Buhari ne ya matsa masa tsayawa takarar gwamna, duk da ba shi da burin yin takara
- Tsohon gwamnan ya ce idan jam’iyyar APC ta kauce daga dabi’unsa, zai koma wata jam’iyya da ke da irin ra’ayinsa
- Ya bayyana cewa zai ci gaba da zama a siyasa har abada, amma ba lallai ne ya ci gaba da tsayawa takara ba a gaba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi magana kan neman takarar gwamna a zaben 2025.
El-Rufai ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ne ya tilasta masa tsayawa takarar gwamna.

Asali: Facebook
Nasir El-Rufai ya magantu kan barin APC
El-Rufai ya bayyana haka ne yayin tattaunawa da tashar Arise TV a daren jiya Litinin 24 ga watan Fabrairun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon gwamnan ya fadi hakan ne yayin da yake nuna yiyuwar sauya sheka daga APC idan har jam’iyyar ta gaza kiyaye manufofinta.
Ya ce kwata-kwata ba shi da buri na siyasa a wancan lokaci inda ya ce a tambayi Buhari da kansa me ya faru, cewar TheCable.

Asali: Twitter
El-Rufai ya fadi rawar Buhari a takararsa
A cewarsa:
“Ba ni da burin yin takara, ku tambayi Buhari, shi ne ya tilasta min tsayawa takarar gwamnan Kaduna saboda ina jin tsoro.”
“Ina da kwarewar aiki, wasu na neman mulki, amma idan an samu matsala, sai su nemi mu gyara, ni, Oby da Ngozi ba mu cika yin yakin neman zabe ba.”
“Bayan da muka kafa APC, Buhari ya ce: ‘Tafi ka tsaya takarar gwamna.’ Na ce, ‘A’a, Malam, ba ni da wannan kwarewar, na fi cancanta a bangaren fasaha.’ Amma ya dage.”
“Mun yi tattaunawa sau da dama kafin na amince, zan ci gaba da siyasa har abada, amma ba na nufin zan ci gaba da yin takara. Idan ba zan samu yadda nake so a APC ba, zan nemi wata jam’iyya.”
El-Rufai daga bisani ya yi fatan shugabannin jam'iyyar APC su yi kokarin gyara kura-kuransu domin kawo sauyi a kasa.
“Ina fatan shugabannin jam’iyyar za su gyara kura-kuransu. Amma yanzu, da dama daga cikinmu ba su ganin APC irin ta da.”
“Idan har APC ba ta gyara kanta ba, zan nemi wata jam’iyya da ke da dabi’u irin nawa domin in ci gaba.”
El-Rufai ya nemo mafita domin ceto Najeriya
Kun ji cewa tsohon gwamnan Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ya sake yin magana kan zaben 2027 da kuma hanyar ceto Najeriya daga halin da take ciki.
Nasir El-Rufai ya ce dole ne Arewa ta hada kai da yankin Kudu maso Kudu don ceto Najeriya daga matsalolin da take fuskanta da kullum ke kara yawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng