El Rufai Ya Kwance Wa Nuhu Ribadu da Uba Sani Zani a Kasuwa, Ya Faɗi Shirin 2031
- Tsohon gwamnan Kaduna, Nasiru El-Rufai ya yi ikirarin cewa mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu na da burin neman takara a 2031
- El-Rufai ya ce hakan ne ya sa Ribadu da Gwamna Uba Sani suka fara kokarin ɓata masa suna da rage tasirin da yake da shi musamman a Arewa
- Kalaman El-Rufai na zuwa ne a daidai lokacin da ake raɗe-raɗin cewa tsohon gwamnan na iya barin APC ya shiga majar da ake shirin yi
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya yi ikirarin cewa mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkonin tsaro, Nuhu Ribadu na da burin neman mulkin Najeriya a 2031.
Malam El-Rufai ya yi ikirarin cewa Ribadu da gwamnan Kaduna na yanzu, Malam Uba Sani suna ta ƙoƙarin ɓata masa suna a idon jama'a ta kowace hanya.

Kara karanta wannan
'Ku tambaye shi, ya sani': El-Rufai ya fadi yadda Buhari ya tilasta masa neman gwamna

Asali: Twitter
El-Rufai ya yi wannan furucin ne yayin wata hira da aka yi da shi a cikin shirin Prime Time na Arise TV a ranar Litinin, 24 ga watan Fabrairu, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
El-Rufai ya yi kaca-kaca da Ribadu, Uba
Tsohon gwamnan ya ce waɗannan mutanen biyu, Nuhu Ribadu da Uba Sani na amfani da hukumar yaƙi da cin hanci watau ICPC suna farautarsa tare da yaransa.
Ya ce su na yin haka ne ba don komai ba sai son su ɓata masa suna a idon jama'a kuma su kassara tasirin da yake da shi a siyasa musamman a Arewacin Najeriya.
Tun bayan barinsa mulki a 2023, El-Rufai ya fara fuskantar bincike kan badakalar kudade a lokacin da yake gwamna.
Haka zalika na zargin cewa rikicin siyasa tsakaninsa da magajinsa, Malam Uba Sani, shi ke kara dagula lamarin.
El-Rufai ya ɓata da Ribadu, Uba Sani
Amma da yake ƙarin haske kan lamarin, Nasiru El-Rufai ya bayyana cewa a yanzu Ribadu da Uba Sani ba abokansa ba ne, kowa ya kama gabansa.
A cewarsa, waɗannan mutane biyu sun fara amfani da ƙarfinsu da duk wani abu da za su iya don ɓata masa suna.
Ya ce suna haka ne saboda mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Ribaɗu na son zama shugaban ƙasa a 2031.

Asali: Facebook
El-Rufai ya yi ikirarin cewa Nuhu Ribadu na ƙoƙarin ɓata sunan da zubar masa da mutunci a idon jama', su daina ganin girmansa.
Ana sa ran dai Arewa za ta karɓi mulkin Najeriya ne bayan Kudu ta yi shekara takwas kan madafun iko kamar yadda tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya yi.
Nasir El-Rufai ya caccaki ƴan siyasa
A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya miƙa sakon godiya ga ƴan uwa da abokan arziki da suka taya shi murnar ƙarin shekara.
Bayan godewa masoya, El-Rufai ya kuma caccaki wasu ƴan siyasa, yana mai cewa ba su yi niyyar tura masa sakon murna ba sai da shugaba Bola Tinubu ya taya shi murna.
Asali: Legit.ng