Malam El Rufai Ya Bayyana Wanda Yake So Ya Karɓi Mulki daga Hannun Tinubu a 2027
- Malam Nasiru Ahmed El-Rufai ya bayyana cewa ya fi son a samu wani daga Kudancin Najeriya ya maye gurbin shugaban ƙasa Bola Tinubu a 2027
- Tsohon gwamnan jihar Kaduna ya ce ba shi da tabbacin zai ci gaba da zama a jam'iyyar APC daga nan zuwa 2027 amma bai yanke shawara ba tukunna
- El-Rufai na ɗaya ɗaga cikin manyan ƴan siyasa a Arewa da ke shirye-shiryen haɗa gamayya domin kifar da gwamnatin Tinubu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa yana so a samu wani dan Najeriya daga Kudu da zai maye gurbin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a 2027.
El-Rufai ya nuna cewa gara a samu wani ɗan Kudu ya karɓi mulkin Najeriya a 2027 ma'ana dai kada shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya yi tazarce.

Asali: Twitter
Malam Nasiru ya bayyana hakan a hirar da aka yi da shi a shirin Prime Time na Arise News ranar Litinin, 24 ga watan Fabrairu, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
El-Rufai na shirin fita daga APC?
Da yake tsokaci kan siyasarsa, El-Rufai ya ce har yanzu bai yanke shawara ba kuma ba shi da tabbacin ci gaba da zama a cikin jam'iyyar APC daga nan zuwa 2027.
Kazalika, ya yi bayani kan zargin cewa Shugaba Tinubu yana fifita yankin Kudu maso Yamma a nade-naden mukamai.
Tsohon gwamnan ya ce ba yankin ne yake fifitawa ba, sai dai mutanen da ke kusa da shi, wato yaransa kaɗai yake bai wa muƙamai a gwamnatinsa.
Tinubu yaransa ya fi ba muƙami
"Abin da ke faruwa shi ne Shugaban Kasa Bola Tinubu ya na ba da mukamai ga mutanensa watau yaransa ba wai don su ‘yan wata kabila ko yanki ba ne," in ji shi.

Kara karanta wannan
"Ba laifin Majalisa ba ne," El Rufai ya fallasa abin da ya sa aka fasa naɗa shi minista
El-Rufai dai na cikin manyan jiga-jigan APC da suka taka rawar gani a kamfen din Tinubu, amma daga baya aka hana shi mukamin minista duk da an tura sunansa Majalisa.
El-Rufai na shirin haɗa gamayya
Malam Nasiru dai na ɗaya daga cikin manyan ƴan siyasar da ake kyautata zaton za su haɗa gamayyar da nufin kayar da Bola Tinubu a babban zaɓe mai zuwa.
Duk da dai har yanzu bai sanar da shirinsa ba amma tsohon gwamnan ya fara ɗasawa da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Asali: Facebook
Wannan ya sa aka fara hasashen zai wahala El-Rufai ya sake tallata shugaban ƙasa Tinubu a karo na biyu, rahoton Leadership.
Amma a hirar da aka yi da shi, Malam Nasiru ya tabbatar da cewa ya fi son a sami wani ɗan Kudu, ya karɓi mulki daga hannun Tinubu a 2027.
Abin da ya hana El-Rufai zama minista
A wani rahoton, kun ji cewa El-Rufai ya musanta zargin cewa ƴan Majalisa ne suka ƙi amince wa da naɗinsa a matsayin minista.
Tsohon gwamnan ya ce Shugaba Tinubu ne ya canza ra'ayi game da naɗinsa, ya fasa aiki da shi a gwamnatinsa.
Asali: Legit.ng