"Ba Laifin Majalisa ba ne," El Rufai Ya Fallasa Abin da Ya Sa Aka Fasa Naɗa Shi Minista

"Ba Laifin Majalisa ba ne," El Rufai Ya Fallasa Abin da Ya Sa Aka Fasa Naɗa Shi Minista

  • Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ce ba Majalisa ba ce ta ƙi tantance shi a matsayin minista
  • El-Rufai ya yi ikirarin cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ne ya canza ra'ayinsa, ya fasa ba shi muƙami a gwamnatinsa
  • Ya ce dama tun farko yana da abubuwan da ya shirya yi bayan ya sauka daga matsayin gwamnan Kaduna amma Tinubu ya dakatar da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa ba Majalisar Tarayya ce ta ƙi amince wa da naɗinsa a matsayin minista ba.

Malam Nasir El-Rufai ya ce shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ne ya canza shawara, ya fasa ba shi muƙami a gwamnatinsa.

Bola Tinubu da Malam Nasiru.
Malam El-Rufai ya zargi Bola Tinubu da fasa naɗa shi a matsayin minista Hoto: Ajuri Ngelale, Nasir El-rufai
Asali: Facebook

El-Rufai ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Arise TV ranar Litinin, 24 ga watan Fabrairun 2025.

Kara karanta wannan

'Ku tambaye shi, ya sani': El-Rufai ya fadi yadda Buhari ya tilasta masa neman gwamna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka fasa naɗa El-Rufai

Tsohon gwamnan wanda ya taka rawa wajen nasarar Bola Tinubu a zaɓen shugaban ƙaar 2023, ya ce ba shi da wata matsala da ƴan Majalisar Tarayya.

Idan za a iya tunawa, bayan miƙa sunayen ministocin farko da Tinubu ya yi a shekarar 2023, majalisa ta daga amincewa da sunan El-Rufai da wasu mutane biyu bisa dalilai da suka shafi tsaro.

Wannan lamari ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, inda ake hasashen cewa Majalisa ce ta yi duk mai yiwuwa wajen hana shi mukamin minista.

El-Rufai: 'Tinubu ne ya canza ra'ayi'

Amma da yake tsokaci kan lamarin yau Litinin, Malam Nasir El-Rufai ya ce ba ruwan Majalisa, Tinubu ne ya canza ra'ayinsa game da naɗa shi muƙami.

"Bayan gama shekara takwas a matsayin gwamna a Kaduna, ina da shiri na, amma shugaban ƙasa a bainar jama'a ya roke ni da na jinkirta shirin da nake yi.

Kara karanta wannan

El Rufai ya kwance wa Nuhu Ribadu da Uba Sani zani a kasuwa, ya faɗi shirin 2031

"Bayan watanni biyu muna tattaunawa, mun cimma matsaya cewa zai naɗa ni a matsayin minista, tare da wasu sharuɗɗa da na gindaya."
"Amma daga baya, ko dai shugaban kasa ya canza ra’ayi ko kuma wani abu ya faru. Amma kada ku yarda da labarin cewa Majalisar Tarayya ce ta ki amincewa da ni.
"Ba su da hannu a lamarin, Shugaban Kasa ne bai so in kasance a gwamnatinsa ba. Ya canza ra’ayi, kuma ni dai ban damu ba, na ci gabaa rayuwata."

- Malam Nasiru El-Rufai.

Malam Nasiru.
El-Rufai ya yi bayani kan rashin naɗa shi minista a gwamnatin Tinubu Hoto: Nasir El-Rufai
Asali: Facebook

El-Rufai ya nuna APC ta gaza

Ya kara da cewa tun bayan abin da ya faru, bai taba yin magana kan gwamnati ba, ko kuma sukar ayyukanta, rahoton Daily Trust.

Sai dai a matsayinsa na wanda ya taka rawa wajen kafa APC, ya ce yana da hakkin yin tambaya kan dalilin da yasa jam’iyyar ta gaza wajen tafiyar da al’amuranta.

Kara karanta wannan

Malam El Rufai ya bayyana wanda yake so ya karɓi mulki daga hannun Tinubu a 2027

2027: El-Rufai ya raba gari da Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa Malam El-Rufai ya bayyana cewa yana so a samu wanu ya maye gurbin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a 2027.

El-Rufai ya ce har yanzu bai yanke shawara ba kuma ba shi da tabbacin ci gaba da zama a cikin jam'iyyar APC daga nan zuwa 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262