"Dole Tinubu Ya Samu Nasara da Ƙarfin Ikon Allah," Minista Ya Hango Abin da Zai Faru a 2027

"Dole Tinubu Ya Samu Nasara da Ƙarfin Ikon Allah," Minista Ya Hango Abin da Zai Faru a 2027

  • Ministan ayyuka, Dave Umahi ya bayyana cewa yana da kwarin guiwar Bola Tinubu zai samu nasara a zaben shugaban ƙasar 2027
  • Tsohon gwamnan jihar Ebonyi ya ce Najeriya na bukatar mutum mai jajircewa irin Tinubu domin kammala ayyukan da ya faro
  • Ministan ya ce da ikon Allah, Tinubu zai samu goyon baya daga ƴan Najeriya a 2027 domin ƙarasa muhimman ayyukan ci gaba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Calabar, Cross River -Ministan ayyuka, Dave Umahi, ya bayyana ƙwarin guiwar cewa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu zai kammala shekaru takwas a mulki.

Umahi, tsohon gwamnan Ebonyi ya nuna haka ne yayin ganawa da masu ruwa da tsaki kan aikin titin Legas zuwa Kalaba a Otal na Eko a jihar Legas ranar Lahadi.

Bola Tinubu da Umahi.
Dave Umahi ya ce Bola Ahmed Tinubu ,zai yi tazarce a 2027 da ƙarfin ikon Allah Hoto: @OfficialABAT
Asali: Facebook

'Dole a sake zaɓen Tinubu a 2027'

Kara karanta wannan

Malam El Rufai ya bayyana wanda yake so ya karɓi mulki daga hannun Tinubu a 2027

Ministan ya jaddada cewa dole ne a sake zaben Tinubu a 2027 da karfin ikon Allah, kamar yadda Channels tv ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Umahi ya ya ce shugaba mai irin jajircewarsa ne kadai zai iya kammala manyan ayyukan ci gaba da Bola Ahmed Tinubu ya fara a faɗin ƙasar nan.

"Mutumin da ke da karfin gwiwar aiwatar da aikin da aka jima ana buri tsawon shekaru 45 da suka gabata, shi ne kawai zai iya kammala shi.
"Ya zama dole ne mu sake zaben Mai girma Tinubu a 2027, da karfin ikon Allah," in ji Umahi.

Gwamnatin Tinubu ta kinkimo ayyuka

Ministan ya yi nuni da cewa gwamnatin Tinubu ta aiwatar da manyan ayyukan bunkasa kasa tun bayan hawanta mulki a 2023, musamman a yankin Kudu maso Gabas.

A cewarsa, waɗannan ayyukan kaɗai za su sanya yankin Kudu maso Gabashin Najeriya ya mara masa baya a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Mutuwa mai yankar ƙauna: Allah ya yi wa mahaifi da kawun ɗan takarar gwamna rasuwa

Umahi ya jaddada cewa gwamnatin Tinubu ta fara ayyukan gina hanyoyi a sassan kasar nan, ciki har da hanyoyin Enugu-Abakaliki da Afikpo-Abia-Okigwe.

"Babu aikin da muka dakatar saboda wata manufa, sai dai muna tabbatar da cewa ana yin komai yadda ya dace.
"Wannan ba a titin Lagos-Calabar kadai yake faruwa ba, har da wasu hanyoyi muhimmai da ake ginawa a fadin kasar nan," in ji shi.
Dave Umahi.
Umahi ya ce Tinubu zai sha ruwan ƙuri'u a zaben 2027 Hoto: Dave Umahi
Asali: UGC

Tinubu zai sha ƙuri'u a Kudancin Najeriya

Umahi, ya ce Shugaba Tinubu ya kawo sauyi mai ma’ana ga yankin Kudu maso Gabas, wanda hakan ke tabbatar da cewa yankin zai mara masa baya a zaɓen 2027.

"Shugaba Tinubu zai samu goyon baya mafi girma daga Kudu maso Gabas saboda irin alherin da ya yi wa yankin.
A zabe mai zuwa, Kudu maso Gabas zai ba shi kashi 99.99% na kuri’u," in ji shi.

Ya kara da cewa gwamnatin tarayya tana cigaba da kokari wajen tabbatar da ci gaban Najeriya gaba daya, yana mai kira ga ‘yan kasar da su goyi bayan Tinubu don kammala abubuwan da ya fara.

Kara karanta wannan

Mutuwa mai yankan kauna: Fitaccen basarake ya rasu, Tinubu ya jajantawa al'umma

An fara kamfen tazarcen Tinubu

Kun ji cewa jam'iyyar APC reshen jihar Kebbi ta fara kamfen neman tazarcen Gwamna Nasir Idris da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a 2027.

Manyan ƙusoshi da suka haɗa da ministoci da jiga-jigan gwamnatin Kebbi sun halarci gangamin da aka gudanar a Birnin Kebbi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262