Kano: APC Ta Rikirkice, Shugaban Jam'iyya Ya Ragargaji Ministan Tinubu
- Jam’iyyar APC ta fusata da barazanar da Karamin Ministan Gidaje da Raya Karkara, Yusuf Abdullahi Ata, ya yi mata
- Shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas, ya bayyana cewa tun da farko ma Yusuf Ata ba cikakken dan jam’iyyar ba ne
- Jikan Sarki ya ce sun yi mamakin yadda Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da korafin su wajen nada Ata Minista
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jihar Kano — Jam’iyyar adawa ta APC reshen jihar Kano ta fusata da barazanar da Karamin Ministan Gidaje da Raya Karkara, Yusuf Abdullahi Ata, ya yi mata.
Ministan ya yi barazanar ficewa daga APC muddin Shugaban Jam'iyyar na Kano, Hon. Abdullahi Abbas, ya sake dawowa a matsayin shugaban jam'iyyar na jihar a karo na hudu.

Asali: Twitter
TABLE OF CONTENTS
A wata hira da BBC Hausa, Shugaban Jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya bayyana cewa tun da farko ma Yusuf Ata ba dan jam'iyyar ba ne.
Ya kuma nuna mamaki kan yadda Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi watsi da shawararsu sannan ya nada Ata a matsayin Minista.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jam'iyyar APC ta fadi dalilin barazanar Ata
Zafafan kalaman Karamin Ministan kan shugabancin APC a wani bidiyo sun ja hankalin ‘yan siyasa a Kano, musamman na jam’iyyar APC.
A martaninsa, Abdullahi Abbas ya ce:
“Mu a wajenmu 'yan jam'iyya, dama ba dan jam'iyya ba ne. A Kano gaba ɗaya, a karamar hukumarsa ne muka yi na uku.
Kuma ba mu sani ba aka ba shi minista, har ma muka gaya wa Shugaban Kasa cewa ba dan jam’iyyarmu ba ne. Ya ci amanar jam'iyya."

Asali: Facebook
Shugaban jam'iyyar APC a Kano ya yi ikirarin cewa wannan shi ne dalilin da ya sa Ministan ke yi musu haka saboda ya san cewa ba dan jam’iyyarsu ba ne.
APC ta yi mamakin nadin Ata a matsayin Minista
Shugaban APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya bayyana mamakinsa kan yadda Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da korafinsu cewa Yusuf Abdullahi Ata bai cancanci zama Minista ba.

Kara karanta wannan
"Ba a shugaban APC zan dawwama ba," Abdullahi Abbas ya fadi kujerar da ya ke nema a kano
Ya ce:
"Muna mamakin yadda aka yi wannan abu, wallahi. Dan siyasa ne kawai na karamar hukuma."
Kalaman Minista da suka tunzura APC
Yusuf Abdullahi Ata ya yi barazanar cewa shi da magoya bayansa za su iya ficewa daga jam'iyyar APC a Kano idan Abdullahi Abbas ya ci gaba da zama shugaban jam’iyya.
A lokacin da yake jawabi ga dandazon jama’a a karamar hukumarsa ta Fagge, Ata ya zargi kalaman Abdullahi Abbas da haddasa wa APC asarar kujerar lamba ɗaya a Kano.
Ya ce:
“An mana tarbiyya, mun san waye malami, mun san waye babba. Saboda haka ba za mu sauka daga turbarmu ba. Idan suka dawo da shi, mu za mu fita. Kuma na rantse da Allah, sai jam'iyyar ta sake faɗuwa a zaɓe.”
"Dole a canja, dole a nemo mutanen kirki masu mutunci a ba su saboda ya zama tare da mu, ya yi sha'awar ya sake ba mu."
APC ta firgita NNPP a Kano
A baya, mun wallafa cewa shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa APC tana shirin tarbar manyan jiga-jigan jam’iyyar NNPP da za su sauya sheƙa.
A lokacin rabon motocin hawa 63 da babura 1,137 ga shugabannin jam’iyyar APC a ƙananan hukumomi da mazabu a Kano, Ganduje ya ce APC ce jam’iyyar da ke da karfi a jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng