Ganduje Ya Firgita NNPP, Ya Fadi Jiga Jigan Jam'iyyar da Za Su Dawo APC

Ganduje Ya Firgita NNPP, Ya Fadi Jiga Jigan Jam'iyyar da Za Su Dawo APC

  • Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa ya nuna cewa manyan ƙusoshi daga NNPP mai mulki a Kano na shirin dawowa APC
  • Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa APC ta shirya tarbar jiga-jigan waɗanda za su sauya sheƙa daga NNPP zuwa cikinta
  • Shugaban na jam'iyyar APC ya kuma ƙwararo yabo ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan manufofin da gwamnatinsa ke aiwatarwa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi magana kan ƴan NNPP da za su sauya sheƙa zuwa APC.

Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa APC tana shirin tarbar manyan jiga-jigan da za su sauya sheƙa daga NNPP, wadda ya bayyana a matsayin jam'iyyar da ta mutu.

Ganduje ya ce jiga-jigan NNPP za su koma APC
Ganduje ya ce APC ta shirya tarbar jiga-jigan NNPP Hoto: @OfficialAPCNg, @KwankwasoRM
Asali: Twitter

Ganduje ya yi wannan bayanin ne a lokacin rabon motocin hawa 63 da kuma babura 1,137 ga shugabannin jam'iyyar APC na ƙananan hukumomi da na mazabu a faɗin jihar Kano, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

'Ina Abba da Kwankwaso?' Yan NNPP ga Sumaila da ya gayyaci Ganduje, Barau

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa aka tallafawa ƴan APC?

Shirin tallafin wanda aka yi domin ƙarfafa jam'iyya da kuma taimakon mambobinta, mataimakin shugaban majalisar dattawa kuma sanatan Kano ta Arewa, Sanata Barau Jibrin ne ya ɗauki nauyinsa.

"Wannan shirin tallafi ba wai ga mambobin APC kawai ba ne, har ma ga al'ummar Kano baki ɗaya. Zai inganta rayuwar jama'a kuma zai ba da damar samun ayyukan yi."

- Abdullahi Umar Ganduje

Kowane shugaban jam'iyyar APC na ƙaramar hukuma zai samu mota, yayin da shugabannin mazaɓu a faɗin mazabu 484 na jihar za su samu babura.

Saboda wasu dalilai, an raba takardun mallakar kayan a wurin taron, tare da umartar waɗanda suka ci gajiyar shirin da su karɓi kayansu daga baya.

Ganduje ya faɗi masu barin NNPP zuwa APC

Ganduje ya yabawa mambobin jam'iyyar bisa ga ƙwazonsu, tare da nuna cewa da yawa daga cikin manyan jami'ai, ƴan majalisa, da sanatoci daga NNPP za su sauya sheƙa zuwa APC nan ba da jimawa ba.

Kara karanta wannan

NNPP ta yi babban rashi, ƙusa a jam'iyyar Kwankwaso ya koma APC

"Dubban mutane suna shigowa babbar jam'iyyarmu. Nan ba da daɗewa ba, za mu tarbi fitattun mutane daga wannan jam'iyyar da ta mutu."

- Abdullahi Umar Ganduje

Haka zalika, Ganduje ya yabawa jagorancin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa gyaran tattalin arziƙi da aka yi ya haifar da raguwar farashin mai, sauƙin farashin abinci, da kuma ƙarfafa darajar Naira.

Sanata Barau zai ci gaba da ba da tallafi

A nasa jawabin, Sanata Barau Jibrin ya bayyana wannan shirin a matsayin farkon wani babban shirin taimako da zai amfani sassa daban-daban na al'umma.

"Wannan babban shiri ne da ya fara da shugabannin jam'iyyarmu. Ta hanyar ba su motocin hawa da babura, muna inganta rayuwarsu kuma muna ƙirƙirar ayyukan yi."

- Sanata Barau Jibrin

Naburaska ya fice daga NNPP zuwa APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa sanannen jarumi a masana'antar fina-finai ka Kannywood, Mustapha Naburaska ya fice daga jam'iyyar NNPP da tafiyar Kwankwasiyya.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi kaca kaca da gwamnatin Tinubu, ya tona makircin da APC ke kullawa a Osun

Naburaska wanda ya koma jam'iyyar APC ta hannun sanata Barau Jibrin, ya bayyana cewa zai ci gaba da ganin girman Gwamna Abba Kabir Yusuf da Rabiu Musa Kwankwaso.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng