Sanata Ya Ki Karbar Tayin Miliyoyi da Mota daga Gwamnan PDP bayan Ya Koma APC
- Sanata Ned Nwoko ya yi biris da tayin da Gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta ya yi masa
- Nwoko ya ce ba zai karɓi mota kirar Land Cruiser da N10m duk wata ba daga Gwamna Sheriff bayan ya koma APC
- Sanata Nwoko ya sauya sheka daga PDP zuwa APC, yana mai cewa mulkin jam’iyyar PDP a Delta ya hana ci gaban siyasa da tattalin arziki na gaskiya
- Sanatan ya kuma ce kafa Jihar Anioma zai kawo ‘yanci ga Delta ta Arewa, yana mai zargin PDP da hana tattaunawa kan hakan don tsare mulkinsu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Asaba, Delta - Sanata Ned Nwoko, mai wakiltar Delta ta Arewa ya magantu kan tayin rufe baki da Gwamna Sheriff Oborevwori ya yi masa.
Sanata Nwoko ya ce ba zai karɓi tayin mota kirar 'Land Cruiser' da N10m kowace wata daga Gwamnan.

Kara karanta wannan
2027: Jigon PDP ya jijjiga tebur, ya fadi abin da ke shirin faruwa da APC a Arewa

Asali: UGC
Sanata ya watsawa gwamna kasa a ido
Nwoko ya bayyana hakan ne a Idumuje Ugboko, Aniocha ta Arewa a yau Lahadi 23 ga watan Fabrairun 2025, cewar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne bayan Nwoko ya koma APC inda ya bayyana cewa jam'iyyar APC ba ta buƙatar gwamnan jiharsa, Sheriff Oborevwori, ya shigo cikinta.
A ranar Laraba, 5 ga watan Fabrairu, 2025 ne Sanata Ned Nwoko ya tabbatar da sauya sheƙarsa daga PDP zuwa APC a wasiƙar da ya miƙawa Majalisar Dattawa.
Sanata ya ce kudaden ba za su amfani mutanensa kai tsaye ba don haka bai gamsu da tayin da aka yi masa ba.
Nwoko ya ce PDP a Delta na kokarin ci gaba da mulki ba tare da gasar siyasa ba, wanda ke hana ci gaban al’umma da tattalin arziki na jihar.
Har ila yau, ya bayyana cewa mulkin PDP a Delta zai kare a 2027, yana mai zargin shugabanninta da fifita kansu fiye da jin dadin jama’a.

Kara karanta wannan
2027: El-Rufai ya fadi yankin da ya dace ya hada kai da Arewa domin ceto Najeriya

Asali: Facebook
Sanata Nwoko ya fadi dalilin komawarsa APC
Nwoko ce ya shiga APC ne don kawo canji, yana mai zargin PDP da hana ci gaba, kuma ya sha alwashin kawo sauyi ta hanyar siyasa mai ma’ana.
Nwoko ya ce kafa Jihar Anioma zai ba Delta ta Arewa ‘yanci daga PDP, amma gwamnatocin baya sun hana tattaunawa kan hakan don kare mulkinsu.
Ya ce da goyon bayan shugabannin APC a matakin jiha da tarayya, kafa Jihar Anioma zai tabbata, kuma hakan zai kawo ‘yanci ga mutanen Delta.
Sanata ya musanta yi wa jaruma ciki
Kun ji cewa Sanata Ned Nwoko daga jihar Delta ya musanta rahoton da ake yaɗawa cewa shi ne uban ɗan cikin da Jaruma Chika Ike ke ɗauke da shi.
Nwoko ya kuma karyata cewa yana shirin auren jarumar masana'antar Nollywood, yana mai cewa labarin da ake yaɗawa ba gaskiya ba ne.
Sanatan ya gargaɗi masu yaɗa jita-jitar da su dakata haka nan domin ba za su cimma burinsu na ɗauke masa hankali ba.
Asali: Legit.ng