El Rufai Ya Sake Dagula Siyasa, Ya Gana da Shugabannin PDP, an Yada Hotuna Ganawar
- Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya gana da shugabannin PDP a sirrance, abin da ya tayar da jita-jitar ficewarsa daga APC kafin zaɓen 2027
- Wasu ‘yan Najeriya na ganin matakin El-Rufai wata dabara ce kan Gwamna Uba Sani, yayin da wasu ke fassara shi a matsayin sauya tsari
- Gwamnatin Bola Tinubu ta zargi El-Rufai da kokarin haddasa rikici a APC, inda mai ba da shawara, Daniel Bwala, ya ce yana neman dagula gwamnati
- Wannan na zuwa ne bayan El-Rufai ya caccaki gwamnatin Bola Tinubu da kuma APC kan yadda suke gudanar da mulkinsu ba tare da tsari ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ya sake tayar da kura game da siyasar Najeriya yayin da ake hasashen ficewarsa daga APC.

Kara karanta wannan
2027: El-Rufai ya fadi yankin da ya dace ya hada kai da Arewa domin ceto Najeriya
El-Rufai ya gana tare da Bashir Saidu da shugabannin jam’iyyar PDP a Kaduna a ranar Talata, 18 ga Fabrairun 2025 wanda ya jawo maganganu kan musabbabin ganawar.

Asali: Twitter
Gwamnatin Tinubu ta dura kan El-Rufai bayan kalamansa
Wani mai amfani da kafar sadarwa, @SafeeyanM shi ya wallafa haka a shafinsa na X a yau Asabar 22 ga watan Fabrairun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Bola Tinubu ta mayar da martani, tana zargin El-Rufai da kokarin haddasa rikici a APC.
Mai ba da shawara kan sadarwa ga shugaban kasa, Daniel Bwala, ya ce:
“Zarge-zargen El-Rufai kan gazawar shugabanci wata dabara ce ta dagula gwamnati.”

Asali: Facebook
Mene dalilin ganawar El-Rufai da shugabannin PDP?
Tsohon gwamnan Kaduna bai ce komai ba game da tuhumar, amma matakinsa na baya-bayan nan na nuna yana shirin wani sabon yunkuri kafin 2027.
Wata majiya da ke da masaniya kan taron ta bayyana cewa:
“Wannan ganawa tana da mahimmanci, har yanzu muna siyasa, don haka ku shirya.”
Har yanzu El-Rufai bai ce komai game da taron ba, amma masana na ganin hakan wata alama ce ta wani sabon shiri kafin zaɓen 2027.Wasu
Jama’a sun tofa albarkacin bakinsu kan wannan al’amari, inda wasu suka nuna farin ciki da yiwuwar sauya sheka.
Martanin wasu masu alaka da kafofin sadarwa
Wani mai amfani da X, @DavidGODsHeart, ya ce:
“Nagari! Dole ne mu kawar da APC daga Aso Rock don amfanin al’ummar Najeriya baki daya.”
@Otunbacashogy2 ya yi martani daban:
“Da tun da wuri ya bar APC, da kyau. Ina da tabbacin mutane da dama za su koma APC saboda shi.”
El-Rufai ya yabawa Atiku kan tattalin arziki
Mun ba ku labarin cewa tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya yabawa Atiku Abubakar a zamanin mulkin Olusegun Obasanjo.
Nasir El-Rufai ya ce tsohon mataimakin shugaban kasar ya taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da gyare-gyaren tattalin arziki a lokacin mulkin daga 1999 zuwa 2007.
A cewarsa, Atiku ne ya jagoranci shirye-shiryen sayar da kadarorin gwamnati, inda El-Rufai ya rike shugabancin BPE, wanda ke karkashin ofishinsa.
Asali: Legit.ng