'Yan Adawa na Kulla Sabon Shiri domin Tunkarar Tinubu da Gaske a 2027

'Yan Adawa na Kulla Sabon Shiri domin Tunkarar Tinubu da Gaske a 2027

  • Jam’iyyun adawa sun fara tuntubar juna da shirye-shiryen sauya dabaru don fuskantar zaben 2027
  • Jiga-jigan adawa sun ce ba batun mukamai ke gabansu ba, sai dai ceto Najeriya daga matsalolin da take ciki
  • Jam’iyyun adawa sun bukaci hadin kai da hakuri domin cimma nasarar kawar da jam’iyya mai mulki

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Yayin da ake tunkarar zaben 2027, jam’iyyun adawa a Najeriya sun fara sabon shiri domin ganin sun samu nasara a babban zabe mai zuwa.

Ana ganin cewa a baya jam’iyyun adawa sun kasa cimma matsaya guda, lamarin da ya bai wa jam’iyya mai mulki damar ci gaba da rike madafun iko.

'Yan adawa
'Yan adawa sun fara maganar tunkarar Tinubu. Hoto: Peter Obi|Atiku Abubakar|Rabiu Kwankwaso
Asali: Facebook

Wani babban jigo daga bangaren adawa ya bayyanawa jaridar Vanguard cewa yanzu ba batun raba mukamai ba ne, sai dai hada kai domin ceton kasa daga kalubalen da take fuskanta.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi ragargaza mai zafi, sun kashe 'yan ta'adda 82, sun kwato tarin makamai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsare-tsare da jam’iyyun adawa ke yi

Masana harkokin siyasa na ganin cewa domin jam’iyyun adawa su yi tasiri a 2027, dole ne su yi gyaran fuska tare da inganta tsarin su na siyasa.

A cewar su, idan har jam’iyyun adawa suka ci gaba da rarrabuwa, hakan zai sa su kara fuskantar matsaloli kamar yadda aka gani a baya.

Baya ga hakan, an bukaci jam’iyyun adawa da su kulla kawance da juna domin su iya hada kai su fuskanci jam’iyyar APC mai mulki.

Wani jigo daga bangaren Atiku Abubakar ya bayyana cewa a yanzu burinsu ba mukamai ba ne, sai dai ganin an ceci kasar daga halin da take ciki.

Bukatar hadin kai a cikin ‘yan adawa

Kakakin jam’iyyar LP, Obiora Ifoh, ya bayyana cewa daya daga cikin kurakuran da aka tafka a 2023 shi ne rashin hadin kan jam’iyyun adawa.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ga ta kansa: An jero manyan ƴan siyasa 17 da suka fice daga jam'iyyar LP

Ya kara da cewa, ba sai an kafa sabuwar jam’iyya ba, domin akwai jam’iyyun da suka nuna karfi kamar LP, wanda a cikin kankanin lokaci ya kawo sauyi a siyasar Najeriya.

A cewarsa, idan har jam’iyyun adawa ba su hade ba, to za su bai wa jam’iyya mai mulki damar yin yadda take so a zabe mai zuwa.

Dabarun da ‘yan adawa ke bukatar dauka

Sakataren CUPP, Cif Peter Ameh, ya bayyana cewa jam’iyya mai mulki ta riga ta shiga cikin lamuran jam’iyyun adawa domin raba su.

A cewarsa, idan har Atiku, Obi da Kwankwaso ba su hakura da burin kashin kansu ba, to za su kara fuskantar matsaloli a siyasa.

Kwankwaso
Shugaba Tinubu da Rabi'u Kwankwaso. Hoto: Bayo Onanuga|Saifullahi Hassan
Asali: Twitter

Ameh ya ce idan ana so jam’iyyun adawa su yi nasara, dole ne su girmama yarjejeniyar karba-karba tsakanin Arewa da Kudu.

Sai dai ya bayyana cewa har yanzu ana da damar ganin jam’iyyun adawa sun hada kai domin su samar da karfi a siyasar Najeriya.

Kara karanta wannan

Rikicin jam'iyyar PDP zai shafi takarar Atiku a zaben 2027? NYFA ta magantu

Abiola ya lashe zaben 1993 - IBB

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban mulkin soja a Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya yi magana kan zaben 1993.

Janar Ibrahim Babangida ya ce MKO Abiola ne ya lashe zaben tare da karin bayani a kan dalilan da suka sanya aka rusa zaben a lokacinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng