Gwamna Ya Yi Kunnen Uwar Shegu da Gargadin Tinubu, Zai Gudanar da Zabe a Jiharsa
- Gwamna Ademola Adeleke ya dage cewa za a gudanar da zaben kananan hukumomin Osun a ranar Asabar, duk da gargadin Atoni-janar na Tarayya
- Adeleke ya ce dimokuradiyya tana bin doka, kuma ba wanda ya isa ya taka dokar kotu inda ya bukaci jama'a su zauna lafiya yayin zaben
- Antoni-janar ya ce zaben ba zai yi inganci ba saboda wa'adin shugabannin kananan hukumomi da kotu ta mayar bai kare ba har zuwa Oktoba 2025
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Osogbo, Osun - Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya bijirewa gargadin gwamnatin Bola Tinubu kan zaben kananan hukumomi.
Gwamna Adeleke ya dage cewa za a gudanar da zaben kananan hukumomi da aka shirya yi a ranar Asabar 22 ga watan Faburairun 2025.

Asali: Twitter
Gargadin Tinubu ga Gwamna Adeleke a Osun
Gwamnatin jihar Osun ita tabbatar da haka a yau Juma'a 21 ga watan Faburairun 2025 a shafinta na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan mataki na zuwa ne duk da rokon Antoni-janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, da a dakatar da shi.
Antoni-janar ya bukaci Adeleke da ya umarci hukumar zaben jihar da ta dakatar da zaben, yana mai cewa hakan ba bisa doka ba ne kuma saba kundin tsarin mulki ne.
Fagbemi ya ambaci hukuncin Kotun wanda ya rushe hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta soke zaben kananan hukumomin da tsohon gwamna Adegboyega Oyetola ya gudanar.
Wannan hukunci ya mayar da shugabannin kananan hukumomin da aka soke, wadanda wa’adinsu, a cewarsa bai kare ba har zuwa Oktoba 2025.
Fagbemi ya ce idan aka yi wani sabon zabe, ba zai yi inganci ba, domin wa’adin sabbin shugabannin da kotu ta mayar yana nan har zuwa Oktoba 2025.

Kara karanta wannan
Gwamna Abba zai jiƙa mutanen Kano da ayyukan alheri, ya ware sama da Naira biliyan 30
Hakan zai zama karara saba wa Kundin Tsarin Mulki, wanda Gwamna Adeleke ya rantse zai kiyaye.
Ya kuma gargadi cewa kada a dauki wani mataki da zai haddasa tashin hankali, yana mai bukatar Adeleke da ya kiyaye doka da tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Gwamna ya sha alwashin gudanar da zaɓe
A cikin sanarwar, mai magana da yawun Gwamna Adeleke, Olawale Rasheed, ya jaddada cewa dimokuradiyya tana tafiya ne bisa doka, kuma babu wanda zai iya yin abin da ya saba wa hukuncin kotu.
“Shawarata ga kowa da kowa, ciki har da masu ruwa da tsaki a matakin kasa da jiha, ita ce su bi ka’idojin dimokuradiyya.
“Ni da mutanena, mun tsaya kan doka, ba kan wani abu na zalunci ba, Za a yi zabe, kuma sakamakon zai kawo ci gaba a matakin kananan hukumomi, Ina kira ga mutanenmu da su zauna lafiya, Osun jiha ce mai zaman lafiya."

Kara karanta wannan
Me ya yi zafi? APC ta sanar da ficewa daga zaben ƙananan hukumomi, ta jero dalilai
- Cewar sanarwar
Osun: APC ta fice daga zaben kananan hukumomi
A baya, kun ji cewa jam’iyyar APC ta janye daga zaben kananan hukumomin Osun da aka shirya ranar 22 ga Fabrairun 2025.
APC ta dauki matakin ne saboda hukuncin kotu da ya mayar da shugabanninta ofisoshinsu a jihar.
Asali: Legit.ng