"Sai Atiku," Ana Tunanin Matsalolin Najeriya Sun Fi Karfin Gwamnatin Tinubu

"Sai Atiku," Ana Tunanin Matsalolin Najeriya Sun Fi Karfin Gwamnatin Tinubu

  • Shugaban ECK Foundation, Dr. Emeka Kalu, ya ce Atiku yana da ƙwarewa da hangen nesa na ceto Najeriya daga rikicin tattalin arziki
  • Kalu ya tabbatar da cewa Atiku na da cikakken tarihin shugabanci da zai kawo gyara ga tattalin arzikin Najeriya domin inganta kasa
  • Ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a Najeriya da su bincika albarkatun ƙasa yadda ya kamata don haɓaka tattalin arzikin ƙasa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Shugaban gidanauniyar ECK, Dr. Emeka Kalu, ya bayyana cewa tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar, shi ne wanda Najeriya ke bukata.

Kaki ya ce a halin yanzu, Atiku ne kadai wanda ke da ƙarfin hali na ceto Najeriya daga mummunan lalacewar tattalin arziki da take ciki idan aka zabe shi a matsayin Shugaban Kasa a shekarar 2027.

Kara karanta wannan

'Najeriya na da arziki': OPEC ta yi fallasa a gazawar kasar a fitar da danyen mai

Atiku
Ana son Atiku Abubakar ya zama shugaban kasa Hoto: @atiku
Asali: Facebook

Vanguard ta wallafa cewa wannan bayani na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka fitar a Legas, inda Kalu ya nuna damuwarsa kan halin da tattalin arzikin ƙasar nan ke ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai, ya bayyana Atiku a matsayin wanda zai kawo canjin da ake muradi domin ya san Najeriya ciki da bai.

An fadi muhimmancin Atiku a Najeriya

Nigerian Tribune ta ruwaito cewa Kalu na da tabbacin Atiku Abubakar yana da hangen nesa da kuma ƙwarewar da ake buƙata domin kauce wa rushewar tattalin arzikin ƙasa gaba ɗaya.

Kalu ya yi suka ga yadda aka sarrafa albarkatun ƙasar ba daidai ba, yana mai nuna bukatar a fito da 'yan Najeriya daga halin tagayyara da suka fada.

Ya yi kira ga ‘yan kasa da shugabannin siyasa da su goyi bayan Atiku domin kawo gyare-gyare da za su taimaka wajen gyara ƙasar.

Atiku: An shawarci ‘yan Najeriya kan shugabanni

Kara karanta wannan

"Raba daidai ake yi," Gwamnatin Tinubu ta ce babu son rai a salon mulkinta

Dr. Emeka Kalu, ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su daina goyon bayan ‘yan siyasa masu cin hanci da rashawa don amfanin kansu.

Atiku
An fara yi wa Atiku Abubakar kamfe Hoto: AbdulRasheeth Shehu
Asali: Facebook

Ya jaddada bukatar a zabi “shugabanni masu kishin ƙasa, wadanda suka cancanta, masu amana, kuma masu ƙwarewa” kamar Atiku domin dawo da ƙasar cikin ƙarfin tattalin arzikin da ta yi a baya.

Ya ce:

“Halin da tattalin arzikinmu ke ciki ya kamata ya tunatar da dukkanin ‘yan Najeriya cewa muna ƙarƙashin shugabancin da ya gaza.
Karuwar yunwa, tsadar rayuwa, faduwar darajar Naira, rashin tsaro, son kai, almundahanar kudi, hauhawar haraji, da rashin aikin yi sun jefa mu cikin matsala mai tsanani.
Kadan daga cikin mafita da za ta kawo dawo da ƙasar kan hanya, shi ne goyon bayan shugabancin siyasa mai ƙwarewa a shekarar 2027.”

Atiku ya soki gwamnatin Najeriya

A baya, kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya zargi APC da ƙoƙarin kwace zaɓen ƙananan hukumomi a Jihar Osun.

A cikin sanarwar da ya fitar, Atiku ya caccaki gwamnatin APC da cewa tana amfani da hanyoyin rashin gaskiya wajen ƙoƙarin kwace zaɓen ƙananan hukumomi a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.