Peter Obi Ya Ga Ta Kansa: An Jero Manyan Ƴan Siyasa 17 da Suka Fice daga Jam'iyyar LP

Peter Obi Ya Ga Ta Kansa: An Jero Manyan Ƴan Siyasa 17 da Suka Fice daga Jam'iyyar LP

  • Jam’iyyar LP na fuskantar koma baya bayan manyan jiga-jiganta sun sauya sheka zuwa APC da PDP, lamarin da ke rage karfinta a siyasance
  • Tsohon dan takarar gwamna, Valentine Ozigbo, ya sanar da ficewarsa daga LP, yana mai cewa ya mika takardar murabus dinsa ga jam’iyyar
  • Jerin wadanda suka fice daga LP na karuwa, wanda ke nuna cewa jam’iyyar na bukatar sababbin dabaru domin ci gaba da haskawa a kasar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tun bayan kafuwarta, jam’iyyar LP ta ke shan fama da kalubale yayin da take kokarin karya karfin APC da PDP da suka mamaye siyasar Najeriya.

Zuwan tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, a Mayu 2022 ya farfado da jam’iyyar, inda ya jawo dimbin magoya baya, musamman matasa.

Jagoran jam'iyyar LP, Peter Obi
Jiga jigan jam'iyyar LP na ci gaba da sauya sheka suna watsar da Peter Obi. Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

LP na fuskantar kalubalen cikin gida

Kara karanta wannan

Rikicin jam'iyyar PDP zai shafi takarar Atiku a zaben 2027? NYFA ta magantu

Tare da Peter Obi, LP ta samu karin shahara, lamarin da ya jawo mutane da dama suka tsaya takara a karkashin jam’iyyar a zabukan 2023, inji rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai bayan zaben, jam’iyyar ta fara fuskantar koma baya, inda wasu daga cikin manyan shugabanninta suka sauya sheka zuwa APC ko PDP.

Sabuwar murabus da aka fi magana a kai ita ce ta tsohon dan takarar gwamna a Anambra, Valentine Ozigbo, wanda ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar.

A ranar Laraba, Legit Hausa ta ruwaito cewa, Ozigbo ya ce ya mika takardar murabus dinsa ga shugaban mazabarsa a Anambra.

Dan takarar gwamna a Anambra, Ozigbo ya sauya sheka zuwa APC daga LP
Dan takarar gwamnan Anambra, Valentine Ozigbo, ya fice daga LP zuwa APC. Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Dan takarar gwamnan Anambra ya fice daga LP

Ozigbo ya tsaya takarar gwamna a 2021 a karkashin PDP, amma daga bisani ya koma LP a watan Agustan 2022 domin mara wa Obi baya.

Baya ga Ozigbo, akwai sauran jiga-jigan jam’iyyar da suka bar LP, inda wasu suka koma PDP yayin da wasu suka sauya sheka zuwa APC.

Kara karanta wannan

Dan takarar gwamna ya canja lissafi, ya sauya sheka zuwa APC ana dab da zabe

Daga cikin kusoshin da suka sauya sheka daga LP akwai 'yan majalisar tarayya da na jihohi, shugabannin jam'iyyar da kuma jiga-jiganta.

Fitattun 'yan siyasa da suka fice daga LP

Ga jerin wasu daga cikin fitattun ‘yan jam’iyyar da suka fice:

  • Valentine Ozigbo
  • Hon. Esosa Iyawe
  • Hon. Dalyop Chollom
  • Alfred Iliya
  • Tochukwu Chinedu Okere
  • Donatus Matthew
  • Bassey Akiba
  • Udengs Eradiri
  • Ezenwa Onyewuchi
  • David Ameh
  • Comrade Isaac Balami
  • Kenneth Okonkwo
  • Erhiatake Ibori-Suenu
  • Doyin Okupe
  • Paschal Obi
  • Lasun Yusuf
  • Olukayode Salako

Ficewar wadannan jiga-jigan siyasa na iya kara dagula LP, musamman ganin yadda jam’iyyar ke kokarin tsayawa da kafafunta bayan zabukan 2023.

Hakazalika, masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin cewa Peter Obi na iya rasa damar da ya samu a zaben 2023 sakamakon ficewar kusoshin jam'iyyar.

'Yan majalisa 27 sun fice daga jam'iyyar LP?

A wani labarin, mun ruwaito cewa, majalisar Legas ta karyata rahotannin da ke cewa ‘yan majalisa 27 sun fice daga APC zuwa jam’iyyar Labour Party.

Kara karanta wannan

NNPP ta yi babban rashi, ƙusa a jam'iyyar Kwankwaso ya koma APC

Shugaban kwamitin yada labarai na majalisa ya bayyana cewa babu wani memba da ke tunanin sauya sheka zuwa wata jam’iyya a yanzu.

Jita-jitar ta bulla ne yayin da majalisar ke fuskantar rikicin cikin gida tun bayan tsige tsohon kakakin majalisar, Mudashiru Obasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.