Tazarce: Minista Ya Fadi Jihar Arewa da Tinubu Zai Samu Ruwan Kuri'u a zaben 2027
- Ministan Gidaje, Arc. Ahmed Dangiwa, ya ce Katsina za ta mara wa Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Dikko Radda baya a zaben 2027
- Dangiwa ya ce Tinubu da Radda sun aiwatar da ayyukan da suka ƙara musu farin jini, wanda zai sa su sha ruwan kuri'u a 2027
- Ministan ya yaba wa jama’a bisa fitowarsu da yawa a zaɓen ƙananan hukumomin da aka gudanar a Katsina, musamman mata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katsina - Ministan gidaje da raya birane, Arc. Ahmed Dangiwa, ya bayyana cewa Katsina za ta mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a 2027.
Dangiwa ya kuma ce Gwamna Dikko Umar Radda zai sake lashe zaɓe a 2027, yana mai cewa nasarorinsu sun tabbatar da cancantarsu ga samun tazarce.

Asali: Twitter
Ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da ‘yan jarida a garin Kankia bayan kada kuri’arsa a zaɓen ƙananan hukumomi, inji rahoton The Nation.

Kara karanta wannan
Gwamna Abba zai jiƙa mutanen Kano da ayyukan alheri, ya ware sama da Naira biliyan 30
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Tinubu, Radda za su samu tazarce' - Dangiwa
Arc. Ahmed ya ce Tinubu da Radda sun yi ayyukan da ba a taba gani ba, lamarin da ya sa ‘yan adawa suka koma kishi da sukar gwamnatocinsu.
“Mutanen Katsina da arewa baki ɗaya za su sake zaɓen Tinubu da Radda saboda manufofinsu sun amfanar da jama’a,” inji Arc. Ahmed.
Dangiwa ya ce duk da sukar ‘yan adawa, shugabannin suna gudanar da ayyukan jin daɗin jama’a da suka ƙara musu farin jini.
Minista ya magantu kan zaben ciyamomin Katsina

Asali: Facebook
Dangane da fitowar masu kada kuri’a, ministan ya jinjinawa jama’a bisa fitowarsu da yawa, yana mai bayyana ranar zaɓen da “rana ta farin ciki.”
“Ko kafin na tafi rumfar zaɓe, an shaida mini cewa jama’a sun fito tun da safe don kada kuri’arsu cikin kwanciyar hankali.”
- Arc. Ahmed.
Ministan ya gode wa jami’an zaɓe da na tsaro, tare da yaba wa mata da suka fi yawa a cikin masu kada kuri’a a zaben ciyamomin jihar na wannan karo.

Kara karanta wannan
Dattawan Arewa sun yaba shirin Tinubu kan Arewa, sun tura muhimmin sako ga gwamnoni
Arc. Ahmed ya ce matan sun nuna ƙwazon gaske, kuma hakan na nuna gamsuwarsu da ayyukan gwamnatoci na ƙasa, jiha, da ƙananan hukumomi.
Katsina: APC ta lashe zaben ciyamomi
A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumar zaɓen Katsina (KTSIEC) ta fitar da sakamakon zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi da aka gudanar a fadin jihar.
Shugaban KTSIEC, Lawal Faskari, ya ce jam’iyyar APC ta lashe dukkan kujerun ciyamomi da kansiloli a zaɓen da aka gudanar ranar Asabar.
Asali: Legit.ng