Rikicin Jam'iyyar PDP Zai Shafi Takarar Atiku a Zaben 2027? NYFA Ta Magantu

Rikicin Jam'iyyar PDP Zai Shafi Takarar Atiku a Zaben 2027? NYFA Ta Magantu

  • Kungiyar NYFA ta ce rikicin cikin gida ba zai hana Atiku Abubakar takara a 2027 ba, kuma ta na nan daram wurin mara masa baya
  • Dare Dada ya bukaci shugabannin PDP da su dauki matakin gaggawa don dakile rikice-rikicen da ke barazana ga makomar jam’iyyar
  • Yayin da PDP ke fuskantar barazanar sauya sheka da murabus din jiga-jigan jam’iyyar, NYFA ta ce ko hakan ba zai shafi Atiku ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Kungiyar matasa masu goyon bayan Atiku (NYFA), ta ce rikicin cikin gida na jam'iyyar PDP ba zai hana Atiku Abubakar yin nasara a 2027 ba.

A wata sanarwa da ta fitar a Lagos a ranar Alhamis, kungiyar ta ce tana nan daram wurin mara wa tsohon mataimakin shugaban kasar baya.

Kara karanta wannan

'Ya aikata laifuffuka 5': An gurfanar da fitaccen mawakin Najeriya a gaban kotu

Matasan NYFA sun yi magana game da matsayin takarar Atiku a 2027 a jam'iyyar PDP
2027: Matasan NYFA sun jaddada cewa rikice-rikicen PDP ba zai shafi takara da nasarar Atiku ba. Hoto: @atiku
Asali: Twitter

NYFA ta koka kan rikice-rikice a PDP

Daraktan hulɗa da jama’a na NYFA, Dare Dada, ya bayyana matsayar kungiyar bayan wani taron da suka gudanar a Lagos ranar Laraba, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dare Dada ya bukaci shugabannin PDP na kasa da su dauki matakin gaggawa domin magance rikicin cikin gida da kuma dawo da hadin kai a jam'iyyar.

“Mun yi nazari kan rikicin da ke faruwa, kuma mun gano cewa wasu ne ke fifita bukatun kansu fiye da jin dadin jam’iyyar,” in ji Dada.

'Rigimar PDP ba za ta hana Atiku takara ba'

Kungiyar NYFA ta nanata cewa Atiku zai yi takara a zaben 2027 karkashin PDP
NYFA ta ce rikicin PDP ba zai shafi takara da nasarar Atiku a 2027 ba. Hoto: @atiku
Asali: Twitter

Ya ce rikice-rikicen baya-bayan nan sun kara nuna gazawar shugabannin, kuma sun rage martabar PDP da aka taba yi wa lakabi da babbar jam’iyya a Afirka.

Dare Dada ya jaddada cewa wadannan rigingimu ba za su hana Atiku takara a 2027 ba, domin yana da shirin inganta rayuwar ‘yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Me ya yi zafi? APC ta sanar da ficewa daga zaben ƙananan hukumomi, ta jero dalilai

Ya ce sauya sheka da murabus din jiga-jigan ‘yan jam’iyyar a yankuna daban-daban na nuna cewa PDP tana cikin mawuyacin hali.

NYFA ta ba shugabannin PDP mafita

Darakta hulda da jama'a na NYFA, yi kira ga wadanda suka amfana da PDP da su daina ruguza hadin kan jam’iyyar saboda son zuciya.

Ya nemi shugabannin PDP da su farka daga barci, domin jam’iyyar na fuskantar barazanar da za ta iya shafar makomarta a 2027.

Dada ya bukaci gwamnonin PDP su hada kai domin yakar masu haddasa rikici da kuma wadanda ke kokarin dagula jam’iyyar.

Ya ce dole ne PDP ta tsaurara hukunci kan masu cin amanar jam’iyya idan tana son samun nasara a 2027.

2027: NYFA ta sake goyon bayan Atiku

A wani labarin, mun ruwaito cewa, kungiyar matasa masu goyon bayan Atiku Abubakar (NYFA) ta ce shi ne dan takarar da zai iya kwato mulki a 2027.

Kara karanta wannan

'Yan Majalisa 27 sun tattara kayansu sun fice daga jam'iyyar APC? an samu bayanai

NYFA ta bukaci 'yan Najeriya su zabi Atiku don farfado da tattalin arziki da bunkasa ci gaban kasa, domin inganta rayuwar al'umma.

Kakakin kungiyar, Dare Dada, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, yana bayani kan wasu manufofin Atiku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.