IBB Ya Yi Fallasa kan Zaben 1993 da aka Rusa, Ya Fadi Rawar da Buhari Ya Taka a Baya

IBB Ya Yi Fallasa kan Zaben 1993 da aka Rusa, Ya Fadi Rawar da Buhari Ya Taka a Baya

  • Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya bayyana cewa marigayi MKO Abiola ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 12 ga Yuni, 1993
  • IBB ya bayyana hakan ne a cikin littafinsa na tarihin rayuwa mai suna A Journey in Service da aka ƙaddamar a birnin tarayya Abuja
  • Tsohon Shugaban Ƙasa Cif Olusegun Obasanjo ya yi kira da a ci gaba da rubuta tarihin rayuwa duk da suka da ake iya fuskanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya bayyana cewa marigayi Cif Moshood Abiola ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga Yuni, 1993.

Ibrahim Babangida ya bayyana hakan ne a cikin littafinsa mai taken A Journey in Service, wanda aka ƙaddamar a Abuja, tare da halartar manyan shugabannin ƙasa.

Kara karanta wannan

"Tinubu mutumin kirki ne, yana da niyya mai kyau," Babban malami ya yi wa mutane Nasiha

IBB Abiola
IBB ya ce Abiola ne ya lashe zaben 1993. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

Daily Trust ta wallafa cewa zaɓen ranar 12 ga Yuni da aka soke na daga cikin mahimman batutuwan siyasa a tarihin Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka zalika Ibrahim Badamasi Babangida ya bayyana cewa hakan na daga cikin ƙalubalen da ya fuskanta a rayuwarsa.

Abiola ne ya lashe zaɓen 1993 – IBB

A yayin ƙaddamar da littafin nasa, Janar Babangida ya bayyana cewa babu shakka MKO Abiola ne ya lashe zaɓen 1993.

A cewarsa, Abiola ya samu mafi yawan ƙuri’u kuma ya cika dukkanin sharudan da ake buƙata don zama shugaban ƙasa.

Janar Ibrahim Babangida ya wallafa cewa:

“Babu tantama a zuciyata, MKO Abiola ne ya lashe zaɓen. Ya cika dukkanin sharuda.”

Ibrahim Babangida ya bayyana cewa yana farin ciki da yadda tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da nasarar Abiola.

IBB ya nuna farinciki kan yadda Buhari ya karrama Abiola da lambar yabo mafi girma ta GCFR, wadda ake bai wa shugabanni.

Kara karanta wannan

Matashi ya gayyaci abokinsa gida ya masa kisan wulakanci da adda, ya sassara shi

IbrahimBabangida ya bayyana cewa yana farin ciki da yadda tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da nasarar Abiola.

Babangida
IBB tare da Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Maganar Obasanjo kan rubuta tarihi

A yayin taron ƙaddamar da littafin, tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya yi kira da a ci gaba da rubuta tarihin rayuwa domin amfanin al’umma.

Ya ce rubuce-rubuce na da matuƙar muhimmanci ga ci gaban ƙasa, kuma yana ba da damar nazari da fahimtar tarihin da ya gabata.

Obasanjo ya bayyana cewa yin rubuce-rubuce kan rayuwa yana iya fuskantar suka daga wasu mutane, amma hakan bai kamata ya hana mutum bayyana labarinsa ba.

Vanguard ta rahoto cewa Obasanjo ya ce:

“Dole ne mutum ya daure, domin ko da ana sukar irin wannan rubutu, hakan yana ƙara nuna muhimmancinsa,”

Shugabanni sun halarci kaddamar da littafin

Taron ƙaddamar da littafin ya samu halartar manyan shugabanni, ciki har da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, wanda ya kasance babban baƙo.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi kaca kaca da gwamnatin Tinubu, ya tona makircin da APC ke kullawa a Osun

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo, shi ne ya gabatar da bitar littafin, tare da tsoffin shugabannin ƙasa irinsu Yakubu Gowon, Abdulsalami Abubakar da Goodluck Jonathan.

Obasanjo ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su cigaba da rubuta tarihin rayuwarsu, domin zai taimaka wajen adana tarihin ƙasa da kuma ilmantar da al’umma kan abubuwan da suka faru a baya.

Peter Obi ya ziyarci IBB a Minna

A wani rahoton, kun ji cewa dan takarar jam'iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi ya ziyarci tsohon shugaban kasa, Ibrahim Babangida.

An ruwaito cewa Peter Obi ya ziyarci Ibrahim Badamasi Babangida ne a gidansa da ke Minna domin karfafa alaka da tsofaffin shugabannin kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng