Dan Takarar Gwamna Ya Canja Lissafi, Ya Sauya Sheka Zuwa APC Ana Dab da Zabe

Dan Takarar Gwamna Ya Canja Lissafi, Ya Sauya Sheka Zuwa APC Ana Dab da Zabe

  • Valentine Ozigbo, dan takarar gwamna a Anambra, ya sauya sheka daga jam'iyyar LP zuwa APC tare da tsohon sakataren jam’iyyar
  • Ozigbo ya bayyana cewa ya fice daga LP ne domin cimma burinsa na ci gaban Anambra, bayan ya sha kaye a 2021 karkashin PDP
  • Bashir Ahmad ya ce sauya shekar Ozigbo alama ce ta rushewar jam’iyyun adawa kafin 2027, yayin da INEC ta shirya zaben Anambra

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Anambra - Dan takarar gwamna a Anambra, Valentine Ozigbo, ya sauya sheka daga jam’iyyar Labour Party (LP) zuwa All Progressives Congress (APC).

A ranar Laraba, tsohon Shugaban Kamfanin Transcorp ya ajiye mukaminsa a LP, yana mai cewa hakan na daga cikin hangen nesansa na ci gaban jihar.

Bashir Ahmed ya yi magana da dan takarar gwamnan Anambra ya sauya sheka zuwa APC
Dan takarar gwamnan Anambra ya fice daga LP, ya koma jam'iyyar APC. Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Anambra: Dan takarar gwamna ya koma APC

Kara karanta wannan

PDP ta fara sayar da fom ɗin takarar gwamnan Anambra, farashin ya jawo cece kuce

Ozigbo ya shiga APC ne a ranar Alhamis tare da tsohon sakataren LP, Nze Afam Okpalauzuegbu, a mazabarsu da ke Amesi, inji rahoton The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A 2021, Ozigbo ya tsaya takarar gwamna a Anambra karkashin PDP, amma ya sha kaye a hannun Chukwuma Soludo na APGA.

Da yake bayyana burinsa na sake takara a 2024, Ozigbo ya ce yana cikin tsarinsa na sauya sheka domin ceton jihar daga durkushewa.

Bashir Ahmad ya yiwa dan takarar maraba

Bashir Ahmad, tsohon hadimin Shugaba Buhari kan sadarwar zamani, ya ce sauya shekarsa alama ce da ke nuna rushewar jam’iyyun adawa nan da 2027.

Tsohon hadimin shugaban kasar ya wallafa a shafinsa na X cewa:

"Mun maraba da Valentine Ozigbo zuwa jam’iyyarmu mai girma, APC. Kafin lokacin fafatawa, dukkanin gungun adawa za su rushe."

Hukumar INEC ta tsara gudanar da zaben gwamna a Anambra a watan Nuwamba 2024.

Kara karanta wannan

Fitar Nabraska a NNPP zuwa APC ya jawo rikita rikita a siyasar Kano

Dan takarar gwamna ya fice daga PDP

Idan ba a manta ba, Legit Hausa ta rahoto cewa, dan takarar gwamnan Anambra karkashin PDP, Valentine Ozigbo ya sauya sheka zuwa jam'iyyar LP.

Valentine Ozigbo, ya ce ba zai iya raba jam'iyya tsakaninsa da Peter Obi ba, wanda ya kira ɗan uwansa, uban gidansa kuma jagora, don haka ya koma LP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.