Gwamna Ya Fara Kamfe, Ya Nuna Wanda Zai Goyi Baya a Zaben Shugaban Ƙasa na 2027

Gwamna Ya Fara Kamfe, Ya Nuna Wanda Zai Goyi Baya a Zaben Shugaban Ƙasa na 2027

  • Jam'iyyar APC reshen jihar Kebbi ta fara kamfen neman tazarcen Gwamna Nasir Idris da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a 2027
  • Manyan ƙusoshi da suka haɗa da ministoci da jiga-jigan gwamnatin Kebbi sun halarci gangamin da aka gudanar a Birnin Kebbi
  • Gwamna Nasir Idiris ya yi ikirarin cewa al'ummar jihar Kebbi suna tare da Bola Tinubu saboda ayyukan alherin da ya zuba masu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kebbi - Jam’iyyar APC a jihar Kebbi ta kaddamar da yakin neman sake zaben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Nasir Idris karo na biyu a zaben 2027.

Taron gangamin, mai taken "Muna Tare da Tinubu da Kauran Gwandu," ya gudana a babban filin wasa na birnin Kebbi.

Kamfen APC.
APC ta fara yakin neman sake zaben Gwamna Nasir Idris na Kebbi da Bola Tinubu a 2027 Hoto: Nasir Idris Kauran Gwandu
Asali: Facebook

Gwamna ya fara kamfen 2027

Gwamna Nasir Idiris na jihar Kebbi ya tabbatar da fara kamfen din a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba zai jiƙa mutanen Kano da ayyukan alheri, ya ware sama da Naira biliyan 30

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manyan ‘yan siyasar suka halarci gangamin sun haɗa da ministan kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki kuma tsohon gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu da Gwamna Nasir Idris.

James Faleke, ƙaramin ministan ilimi, Yusuf Tanko Sununu, da sauran manyan jami’an gwamnati sun halarci wannan gangamin yaƙin neman zaɓe.

An fara kamfen Tinubu da Nasir Idris

Da yake jaabi, Sanata Atiku Bagudu ya ce Shugaba Tinubu da Gwamna Idris sun yi abin a zo a gani cikin kasa da shekaru biyu, don haka ya dace a sake zabarsu wa'adi na biyu.

"Gwamnatin Tinubu ta yi kokari sosai wajen inganta Najeriya. Shugaban ƙasa ya cika alkawuran da ya daukarwa jihar Kebbi, kuma ina alfahari da kasancewa tare da shi," in ji Bagudu.

Ya lissafa manyan ayyukan da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa a Kebbi, ciki har da titin Natsini-Kangiwa-Kamba (wanda aka kaddamar da shi akan Naira biliyan 35).

Bagudu ya kuma ambaci aikin titin Malamfari-Ngaski-Warah, babban titin Sokoto-Kebbi-Badagry da titin Koko-Mahuta-Dabai a cikin ayyukan da Tinubu ke yi.

Kara karanta wannan

"Raba daidai ake yi," Gwamnatin Tinubu ta ce babu son rai a salon mulkinta

Ya kuma sanar da bada tallafin Naira miliyan 450 ga mazabu 225 na jihar Kebbi don sayen kayan abinci da rabawa mabukata kafin watan Ramadan.

2027: Mutanen Kebbi na tare da Bola Tinubu

A nasa jawabin, Gwamna Nasir Idris ya ce mutanen Kebbi suna tare da Tinubu saboda ayyukan ci gaba da ya kawo wa jihar.

"Mutanen Kebbi na tare da Shugaba Tinubu saboda ya kawo mana ci gaba. Idan lokacin ya yi a 2027, za mu gani idan wani zai ce yana da magoya baya fiye da Tinubu a Kebbi," in ji Gwamnan.
Gwamna Idris.
An fara kamfen gwamna da shugaba Bola Ahmed Tinubu a jihar Kebbi Hoto: Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu
Asali: Facebook

PDP ta mutu a jihar Kebbi

Shugaban majalisar dokokin jihar Kebbi, Muhammad Usman Zuru, ya bayyana cewar jam’iyyar adawa ta PDP ta rasa duk wani tasiri a siyasar jihar, yana mai cewa jam’iyyar ta mutu murus.

Ya ce jam’iyyar APC ce kadai ke da rinjaye a Kebbi, domin mafi yawan jiga-jigan PDP, wadanda ke da kishin kasa da tasiri a siyasa, sun fice daga jam’iyyar tare da komawa APC domin ci gaban jihar.

Kara karanta wannan

"Tinubu mutumin kirki ne, yana da niyya mai kyau," Babban malami ya yi wa mutane Nasiha

A cewarsa:

"Masu faɗa a ji da kishin kasa a PDP duk sun koma APC don ci gaban Kebbi. Jam’iyya daya ce kawai ta rage mana kuma, ita ce APC."

Ya bayyana hakan ne yayin wani taron jam’iyyar da aka gudanar, inda aka tattauna kan ci gaban jam’iyyar da shirye-shiryen da take yi na kara samun karbuwa a zukatan al’ummar jihar.

A cikin wannan taro, gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya sanar da cewa an ware motocin yakin neman zabe guda 21, domin rabawa kowace karamar hukuma a fadin jihar.

Wannan mataki, a cewarsa, zai taimaka wajen saukaka aikin wayar da kan jama’a da kuma yada manufofin jam’iyyar APC ga jama’a a yankunan karkara da birane.

A cewar gwamnan, wannan mataki yana daya daga cikin dabarun tabbatar da cewa APC ta ci gaba da samun goyon bayan jama’a, domin cigaban jihar da al’ummarta.

Gwamnan Kebbi ya kori mutum 21

Kara karanta wannan

'Yan Shi'a fusata, sun ta aika kakkausan sako ga gwamnatin Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Kebbi ya fara garambawul a ɓangaren ilimi, ya kori shugabannin ilimi a ƙananan hukumomi 21.

Nasir Idris ya gode masu bisa gudummawar da suka bayar tsawon lokaci, kana ya bukaci su iƙa ragamar jagoranci ga daraktoci a hukumominsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262