Kakakin Majalisa Ta Ji Wuta, Ta Yi Murabus daga Muƙaminta? Bayanai Sun Fito
- Kakakin Majalisar dokokin jihar Legas, Hon. Majisola Meranda ta musanra raɗe-raɗin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa ta yi murabus
- Babban sakataren watsa labaran kakakin, Segun Ajiboye ya tabbatar da cewa Hon Meranda tana ofishinta tana ci gaba da ayyukan da ke gabanta
- Majalisa ta tsunduma cikin rikici ne bayan tsige Hon. Mudashiru Obasa daga matsayin shugaba tare da maye gurbinsa da Meranda
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Lagos - Kakakin Majalisar Dokokin jihar Legas, Hon. Mojisola Meranda, ta musanta rahotannin da ke yawo cewa ta yi murabus daga mukaminta.
Hon. Meranda, mace ta farko da Allah ya ba matsayin shugaban Majalisar dokokin a tarihi, ta ce ba ta yi murabus ba kuma tana nan tana ci gaba da ayyukan ofishinta.

Asali: Twitter
Babban sakataren watsa labaranta, Segun Ajiboye, ne ya yi karin haske kan batun a wata hira da wakilin jaridar Punch Online a ranar Laraba, 19 ga watan Fabrairu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin Majalisar Legas tana kan aiki
"Yanzu haka in na ofis, kuma ita ma kakakin majalisar tana nan a ofishinta. Ban san daga inda wannan jita-jita ta fito ba," in ji Ajiboye.
Wasu rahotanni da suka bazu a kafafen sada zumunta sun yi ikirarin cewa Meranda ta ajiye mukaminta.
Haka nan, wata takarda mai ɗauke da kwanan wata 17 ga Fabrairu, 2025, da ake dangantawa da ita ta yadu tsawon kwanaki biyu.
Daga ina jita-jitar ta samo asali?
A cikin takardar, an yi zargin cewa Hon. Meranda ta sanar da murabus dinta a hukumance, ta ajiye mukamin kakakin Majalisar dokokin Legas.
Duk da haka, bincike ya nuna cewa takardar ba ta dauke da sa hannun kowa, wanda hakan ke nuna cewa akwai shakku game da sahihancinta.
Yadda wutar rikici ta kama a Majalisar
Tun bayan tsige tsohon kakakin majalisa, Mudashiru Obasa, majalisar ta tsinci kanta cikin rikicin shugabanci wanda har yanzu bai kare ba.

Kara karanta wannan
Ajali ya yi: Sanata ta riiga mu gidan gaskiya bayan an mata tiyata a ƙasar Amurka
Hon. Obasa, wanda ya rike mukamin kakakin majalisar tsawon shekaru, an tsige shi ne sakamakon rashin jituwarsa da yawancin ‘yan majalisa, rahoton The Nation.

Asali: Twitter
Kakakin Majalisar Legas na nan daram
Meranda, wacce ta karbi ragamar shugabanci, tana fuskantar kalubale daga wasu bangarorin siyasa, wanda hakan ke kara janyo jita-jita da rade-radi game da kujerarta.
Sai dai duk da haka, ta ci gaba da gudanar da ayyukanta, tana mai jaddada cewa babu wani abu da zai tilasta mata yin murabus.
Atiku ya sa baki a rikicin Majalisar Legas
A wani rahoton, kun ji cewa Alhaji Atiku Abubakar ya caccaki jami'an tsaro bisa mamayar da suka kai zauren Majalisar dokokin jihar Legas.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya zargi Shugaba Tinubu da hannu dumu-dumu a lamarin, ya kuma bukaci a gudanar da sahihin bincike.
Asali: Legit.ng