'Yadda El Rufai Ke Yi Wa Siyasarsa Illa bayan Rikito Rigima da APC, Ribadu da Uba Sani'
- An bayyana rigimar da Nasir El-Rufai ke yi da Gwamna Uba Sani, APC, da NSA Nuhu Ribadu ka iya lalata masa siyasa
- Masanin siyasa, Kelly Agaba, ya ce hakan na iya shafar siyasar El-Rufai a 2027 duba da shirin haɗaka da yake yi
- Agaba ya ce sukar El-Rufai ga jagorancin APC da matsalolinsa da Uba Sani da Ribadu na iya nisantar da shi daga manyan jiga-jigai a jam’iyyar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, yana cikin rikice-rikice da Gwamna Uba Sani, jam’iyyar APC mai mulki, da NSA Nuhu Ribadu.
Wani masanin siyasa, Kelly Agaba, ya bayyana yadda hakan zai iya shafar siyasarsa a 2027 da gaba.

Source: Facebook
An fadawa El-Rufai illar da yake yiwa siyasarsa

Kara karanta wannan
Malamin addini ya shiga siyasa a Kano, ya jagoranci magoya bayansa zuwa jam'iyyar APC
A wata hira da Legit.ng, Agaba ya ce sukar El-Rufai ga jagorancin APC da matsalolinsa da Uba Sani da Ribadu na iya nisantar da shi daga manyan jiga-jigai a jam’iyyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Agaba ya ce fuskantar rikice-rikice da yawa lokaci guda yana da hatsari a siyasar Najeriya.
Ya ce hakan na iya rage wa El-Rufai karfi a jam'iyyar APC da ya sha mata wahala tun farko.
Yayin da yake mayar da martani kan kalaman El-Rufai game da APC, Uba Sani, da Nuhu Ribadu, masanin ya ce irin wadannan kalamai suna ta da cece-kuce.
"Maganganun El-Rufai kan APC, Gwamna Uba Sani da Nuhu Ribadu sun haddasa mahawara sosai, fuskantar rikice-rikice da yawa lokaci guda na da hadari a siyasar Najeriya."
"Tsokacin El-Rufai kan shugabancin APC da matsalolinsa da Uba Sani da Ribadu na iya nisantar da shi daga jiga-jigai a jam’iyyar, hakan na iya shafar siyasarsa a 2027."
Cewar Agaba
Matsalar da El-Rufai ka iya fuskanta a siyasarsa
Da yake magana kan illar fuskantar rikice-rikice da yawa, Agaba ya ce hakan na iya dagula alakarsa da manyan ‘yan siyasa.
Masanin ya ce hakan na iya hana El-Rufai samun goyon baya a gaba wanda ka iya shafar burinsa a nan gaba.
El-Rufai: An dura kan Gwamna Uba Sani
Kun ji cewa Gwamna Uba Sani ya taya tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai murnar zagayowar haihuwarsa, inda ya yi masa fatan alheri.
Sai dai sakon taya murnar ya jawo ka-ce-na-ce a kafofin sadarwa bayan rade-radin rashin jituwa tsakaninsu.
Asali: Legit.ng
