"Za Mu Kawo Karshen Mulkin Kama Karya," PDP Ta Musanta Baraka a Cikinta
- PDP ta ce babu wani fifiko da Ambasada Umar Iliya Damagum ke yi wajen nadin sabon Sakataren jam'iyyar na kasa
- A cewar hadimin mukaddashin shugaban PDP, Yusuf Dingyadi, wasu daga Arewa ne ke kokarin kara rarraba kan 'yan jam'iyya
- Ya kara da cewa yanzu manufar da ta dace da su bai wuce yadda za a hada kai wajen ceto Najeriya daga mulkin da APC ke yi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja — Jam’iyyar adawa PDP ta yi watsi da zarge-zargen da ke cewa Mukaddashin Shugaban Jam’iyyar na Kasa, Umar Iliya Damagum, yana nuna son kai wajen zabar sabon Sakatare.
Mataimakin na Musamman kan Harkokin Yada Labarai da Sadarwa na Shugaban PDP na Kasa, Yusuf Dingyadi ne ya musanta zargin a sanarwar da ya raba ga manema labarai.

Asali: Facebook
Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito cewa Dingyadi ya ce Ambasada Damagum yana kokarin hada kan ‘ya’yan jam’iyyar tare da karfafa shugabancinta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana zarge-zargen da ake yi wa shugaban a matsayin marasa tushe da makama, yana mai cewa wasu tsiraru ne ke kokarin haddasa rabuwar kai.
“Babu baraka tsakanin Damagum da Anyanwu,” PDP
Dingyadi ya bayyana cewa Ambasada Damagum ba ya Abuja a ranar da Sanata Samuel Anyanwu ya kama aiki a hedkwatar PDP ta kasa, wanda shi ne dalilinsa na rashin halartar taron.
Ya shaida wa legit cewa ana kokarin dora wa mukaddashin shugaban PDP irin wadannan kalamai ne saboda son rai.
Dingyadi ya zargi wasu daga 'yan Arewacin kasa da kitsa irin wannan labari, a kokarin kakabawa jam’iyyar shugabanci da zai kare muradunsu ta hanyar murkushe ‘yan adawa na cikin gida.
PDP: “Babu alaka tsakanin Damagum da Wike”
Da yake mayar da martani kan rade-radin da ke cewa Damagum yana da alaka da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, Dingyadi ya karyata hakan, yana mai cewa Damagum yana nan daram cikin biyayyarsa ga PDP.

Kara karanta wannan
Dattawan Arewa sun yaba shirin Tinubu kan Arewa, sun tura muhimmin sako ga gwamnoni
Ya ce:
“Muna ta kokarin ganin cewa yanzu an hada kai, an samar da ingantaccen tsarin da jam’iyyar PDP za ta bi domin yaki da wannan mugu abin da ake ciki na mulkin kama karya.”
Dingyadi ya bayyana cewa matukar PDP ba za ta hada kanta waje guda ba, akwai barazana ga burinta na ceto ‘yan Najeriya daga mulkin APC.
PDP na shirin kwace mulki daga APC
PDP ta bukaci daukacin 'yan jam'iyyar da su watsar da adawa ta cikin gida domin tabbatar da shirin da ake yi na raba APC da mulkin Najeriya a kakar zabe mai zuwa.
Yusuf Dingyadi ya bayyana cewa APC ta na mulki ne da isa da take hakkin 'yan kasa, wanda ya sa dole ne a yi fafutukar samar wa jama'a 'yanci a 2027.
PDP ta caccaki wasu 'yan majalisa
A wani labarin, mun ruwaito cewa jam’iyyar PDP ta bukaci dukkan ‘yan majalisar wakilai da na majalisar dokokin jihar Kaduna da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki da su ajiye mukamansu.
A ranar Asabar ne wasu daga cikin ‘yan majalisar daga kudancin Kaduna suka kasance cikin jerin mutane 50 da suka sauya sheka zuwa APC, lamarin da PD ke ganin ya saba doka su tafi da mukamansu.
Asali: Legit.ng