Atiku Ya Yi Kaca Kaca da Gwamnatin Tinubu, Ya Tona Makircin da APC Ke Kullawa a Osun

Atiku Ya Yi Kaca Kaca da Gwamnatin Tinubu, Ya Tona Makircin da APC Ke Kullawa a Osun

  • Atiku Abubakar ya zargi jam'iyyar APC da yin amfani da 'yan daba a yunkurin kwace zaɓen ƙananan hukumomi a Osun
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi ikirarin cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na ƙoƙarin murƙushe tsarin dimokraɗiyya
  • Atiku ya nemi hukumomin tsaro su guji goyon bayan APC, inda ya ce Najeriya na bukatar shugabanci nagari ba siyasar rigima ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya zargi APC da yunƙurin kwace zaɓen ƙananan hukumomi a Osun.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana haka a wata sanarwa da ya wallafa a shafukan sada zumunta.

Atiku ya yi magana kan rikicin siyasa da ya barke a jihar Osun.
Atiku ya caccaki gwamnatin APC kan yunkurin kwace zaben kananan hukumomin Osun. Hoto: @atiku
Asali: Twitter

Atiku ya zargi APC da son kwace Osun

A sanarwar da Legit Hausa ta gani a shafin Atiku na dandalin X, tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce:

Kara karanta wannan

2027: 'Yan adawa za su yi taron hadin kai domin tunkarar APC da murya daya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"APC ta ƙaddamar da farmaki kan tsarin dimokraɗiyya, tana ƙoƙarin kwace zaɓen ƙananan hukumomi ta hanyar amfani da karfi."

Ya ƙara da cewa ba za a tilasta wa Osun miƙa wuya ga masu adawa da dimokraɗiyya ba, yana mai cewa Shugaban kasa Bola Tinubu da tawagarsa su daina siyasar tada zaune tsaye.

"Yan Najeriya sun shaida yadda APC ta nuna yadda take son riƙe mulki ko ta wane hali, tana fakewa da tashin hankali."

- Atiku Abubakar.

Atiku ya jinjinawa jajurcewar 'yan Osun

A cikin sanarwar, Atiku ya ci gaba da cewa:

"A Osun, APC ta aika da 'yan daba don ƙwace ikon ƙananan hukumomi 30, yayin da gwamnati ke kallon abin yana faruwa.
"Idan ba saboda jarumtakar mutanen Osun ba, da dimokraɗiyya a jihar ta faɗa hannun 'yan siyasar da ke son mulki ko ta halin kaka.
"Ya zama dole a fahimta cewa Osun ba za ta yarda a tauye mata haƙƙinta na zaɓe ba, duk da barazana da ake yi."

Kara karanta wannan

Cacar baki ta balle tsakanin APC, NNPP kan yi wa gwamnatin Abba Gida Gida kishiya

Tsohon dan takarar shugaban kasar ya ci gaba da cewa:

"Muna kira ga hukumomin tsaro da su tabbatar da yin aikinsu bisa doka ba tare da bari APC ta yi amfani da su don cimma manufarta ba.
"Wannan lokaci ne mai hadari, APC ta nuna babu wata damuwa da take da ita game da dimokraɗiyya, illa kawai riƙe mulki ta kowace hanya."

Atiku ya gargadi Tinubu da jam'iyyar APC

Atiku ya yabawa mutanen Osun bisa jajircewarsu wajen kare dimokraɗiyya daga abin da ya kira danniya.

"Mun yaba da jarumtar mutanen Osun da suka ƙi yarda a murƙushe su. Jajircewarsu alama ce ta fata a lokacin da ake zalunci.
"APC ta Tinubu ta nuna a fili cewa ba ta damu da ra'ayin jama'a ba. Amma dole ne 'yan Najeriya su ƙi yarda da hakan.
"Tinubu da mabiyansa su daina siyasar tada zaune tsaye, ba kawai a Osun ko Legas ba, har ma a duk ƙasar.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi magana kan takaddamar filin BUK, ya aika sako ga Gwamna Abba

"Mutane na buƙatar shugabanci nagari, ba rikici da tashin hankali ba. Ba za mu kyale a tauye dimokraɗiyya ba."

- Atiku Abubakar.

An kashe mutane 6 a rikicin siyasar Osun

A wani labarin, mun ruwaito cewa, rikicin siyasa da ya ɓarke a jihar Osun bayan hukuncin kotu da ya yi sanadin mutuwar akalla mutane shida.

Gwamna Ademola Adeleke ya dora alhakin rikicin kan ministan tattalin arzikin ruwa, Gboyega Oyetola, da jami’an tsaro, yana zarginsu da haddasa tashin hankali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.