"Ba Sabani aka Samu ba," Naburaska Ya Fadi Dalilin Watsi da Kwankwasiyya

"Ba Sabani aka Samu ba," Naburaska Ya Fadi Dalilin Watsi da Kwankwasiyya

  • Fitaccen dan Kannywood, Mustapha Naburaska ya musanta cewa ansamu rikici ko sabanin akida da shi a tafiyar Kwankwasiyya
  • Ya bayyana cewa ya koma APC a inuwar Barau I Jibrin saboda biyan bukatar kashin kai da samar da ci gaba ga kasuwancinsa
  • Dan wasan kwaikwayon ya ce da shigar sa APC, ya kara samun damar yi wa manufofin gwamnati talla da samun sabon mukami

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar KanoFitaccen dan Kannywood, Mustapha Naburaska ya bayyana dalilan da suka sa ya ajiye jar hularsa, tare da rungumar tafiyar Barau I Jibrin.

Ya musanta zargin cewa ba wai an samu sabanin akida ko wani rikici da shi a NNPP ba, wanda shi ne ya sa ya tilasta ajiye jar hularsa zuwa APC.

Kara karanta wannan

'Ba shi da tsoro ko kadan': Abin da Tinubu ya ce bayan babban rashin da Najeriya ta yi

nabur
Naburaska ya fadi dalili rungumar APC Hoto: Barau I Jibrin
Asali: Facebook

A wata hira da ta kebanta da DCL Hausa, Naburaska ya tabbatar da cewa ba wai bai mori NNPP ba ne, sai dai akwai wani dunkulellen alheri da ya tunkaro shi daga tafiyar Barau.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Naburaska ya fadi wanda ya ja shi APC

Dan wasan kwaikwayon Kannywood, Mustapha Naburaska, ya bayyana cewa ubangidansa, Sanata Ibrahim Lamido, mai wakiltar Sakkwato ta Gabas, ne ya masa hanyar shiga tawagar Mataimakin Shugaban Majalisa, Barau I Jibrin.

Ya bayyana cewa Sanata Lamido ya yi masa hanyar sama da babban mukami a tafiyar Barau, inda yanzu haka aka yi masa mukamin mashawarci a kan wayar da kan jama’a.

Naburaska ya ce:

"Idan aka ce za a yi aiki, za a ba ka wani yanki da za ka ci gaba da harkokinka, ba yana nufin za ka bar wani ka koma wajen wani ba ne. Shi wanda ya ce zo ka ci tuwo ai ya fi tuwon dadi."

Kara karanta wannan

An gano dalilin faduwar farashi a shahararriyar kasuwar abinci a Kano

Dan fim din ya kara da cewa kamfaninsa yana samun tagomashin kwangila wajen tallata al’amuran da suka shafi kasa daga tafiyar Barau, saboda haka ne ya rungumi tafiyar.

"Menene mukami na a Kwankwasiyya?" - Naburaska

Mustapha Naburaska ya bayyana cewa zai ci gaba da mutunta Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir Yusuf, amma bai samu irin mukamin da yake rike da shi a tafiyar Barau ba.

Ya nanata cewa ba wai bai samu wani abu a gwamnatin Kwankwasiyya a Kano ba, amma bai kai tagomashin da yake samu a tafiyar Barau I Jibrin ba.

Naburaska ya kara da cewa:

"Walla Allah can kuka ce, kuma ina son canji, shi yasa."

Ya kara da cewa yana zuwa wajen Barau ya samu canjin da yake bukata, ciki har da samun tallace-tallace da mukamin da zai tafi da duk wani dan Najeriya, ba sai ‘yan APC ba kadai.

Naburaska ya koma APC

Kara karanta wannan

"Bai dace gwamnati ta nade hannayenta ba": Ndume ya nemi majalisa ta duba zargi kan USAID

Kun samu labarin cewa Wasu shahararrun ‘yan wasan Kannywood sun fita daga jam’iyyar NNPP zuwa APC a jihar Kano, lamarin da ke nuna sauyin lamuran siyasa a yankin.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Barau I. Jibrin, ya ce matakin ya nuna yadda jam’iyyar APC ke ƙara samun karɓuwa a jihar Kano da ma Najeriya baki ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.