2027: 'Yan Adawa Za Su Yi Taron Hadin Kai domin Tunkarar APC da Murya Daya

2027: 'Yan Adawa Za Su Yi Taron Hadin Kai domin Tunkarar APC da Murya Daya

  • Daraktan NCFront, Wale Okunniyi ya bayyana shirin kafa gagarumin haɗin gwiwa domin kayar da APC a zaɓen 2027
  • Ya ce za su ƙirƙiri wata sabuwar babbar ƙungiya ta siyasa ta hanyar haɗa jam’iyyu da canza tsarin shugabancinsu
  • Okunniyi ya tabbatar da cewa ana ci gaba da tattaunawa da manyan ‘yan siyasa ciki har da Atiku Abubakar da Peter Obi
  • Legit ta tattana da wani matashi dan jam'iyyar PDP domin jin yadda yake ganin shirin hadakar za ta kasance

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Darakta-Janar na NCFront, Wale Okunniyi ya bayyana cewa ana kokarin kafa sabon babban haɗin gwiwar siyasa domin kalubalantar jam’iyyar APC a zaɓen 2027.

Wale Okunniyi ya ce za su dawo da dabarun da suka yi amfani da su a baya wajen kawar da mulkin jam’iyya ɗaya, domin tabbatar da gaskiya da adalci a siyasar Najeriya.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi kaca kaca da gwamnatin Tinubu, ya tona makircin da APC ke kullawa a Osun

Atiku
Ana shirin taron 'yan adawa domin tunkarar APC a 2027. Hoto: Atiku Abubakar|Bola Tinubu|Mr Peter Obi
Asali: Facebook

Punch ta wallafa cewa Okunniyi ya ce za su zaɓi wata jam’iyya daga cikin PDP, NNPP ko LP, su haɗa ƙarfi, su sabunta ta, tare da haɗa duk wasu ‘yan siyasar da ke son kawo sauyi a ƙasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kokarin kafa tafiyar siyasa domin 2027

Okunniyi ya bayyana cewa shirin su ba wai kawai ƙirƙiro wata ƙaramar jam’iyya ba ne, sai dai su haɗa ƙarfi da wata jam’iyya da ta shahara, su canza tsarin shugabancinta don cimma burinsu.

Dan siyasar ya ce:

"Ba za mu jira INEC ta yi mana rajista ba. Idan har ba ta yi ba, to, za mu ɗauki wata jam’iyya, mu canza tsarin ta, mu haɗa ƙarfi da ‘yan siyasar da ke son sauyi."

Ya kara da cewa tun a shekarar 2023 suka fara wannan shiri, tare da goyon bayan masana da manyan ‘yan siyasa irin su Attahiru Jega, Prof. Pat Utomi da Oby Ezekwesili.

Kara karanta wannan

"Menene hujjar ku?" PDP ta karyata kitsa kai wa APC hari a Zamfara

A cewar Okunniyi, tun daga watan Fabrairu na shekarar 2023, suka fara tsara yadda za su samar da gagarumin haɗin gwiwa domin kafa sabuwar gwamnati da za ta ceto Najeriya.

'Yan siyasa za su haɗu a watan Mayu

Okunniyi ya tabbatar da cewa ana ci gaba da tattaunawa da manyan ‘yan siyasa irin su Atiku Abubakar da Peter Obi domin su shiga cikin sabon tsarin.

"Ana tattaunawa da kowa, kuma za mu haɗa kai a wani babban taro da ake shirin gudanarwa a watan Mayu.
"Idan muka zaɓi wata jam’iyya, za mu tattauna da shugabanninta domin sabunta tsarin su."

Ya ce wannan yunƙuri ba wai domin samun mulki kawai ba ne, sai dai domin kawo tsarin siyasa mai dorewa da zai ceto ‘yan Najeriya daga wahalhalun da suke ciki.

Shin Arewa na cikin tafiyar?

Wale Okunniyi ya tabbatar da cewa yankin Arewa yana da babbar rawa a wannan shiri, yana mai cewa hatta wasu manyan ‘yan APC na nuna sha’awa.

Kara karanta wannan

Cacar baki ta balle tsakanin APC, NNPP kan yi wa gwamnatin Abba Gida Gida kishiya

"A yanzu Arewa na da fiye da kashi 50 cikin 100 na mutanen da ke goyon bayan wannan yunƙuri. Mun fahimci cewa su ma sun gaji da halin da ake ciki."

Ya ce gwagwarmayar ba wai a kan mutum ɗaya take ba, sai dai akan ceton Najeriya daga matsalolin da ke addabar ta.

Ya kuma yi bayani kan yadda za su samar da sabuwar gwamnati da ke da tsare-tsaren da za su amfani talakawa.

Legit ta tattauna da dan PDP

Wani matashi dan jam'iyyar PDP a jihar Gombe, Aminu Isa ya ce kokarin abu ne mai kyau lura da halin da 'yan adawa ke ciki.

"Idan aka lura da yadda APC ta karbi mulki a 2015, za a fahimci cewa hadaka abu ne mai kyau a tsakanin 'yan adawa.
'Ina fata hakan zai zamo dalilin kawo mulkin da zai sauya lamura a Najeriya."

Kara karanta wannan

Gwamna ya lissafa dalilan da za su sanya talaka zaben Tinubu a 2027

2027: Dogara ya ba Tinubu shawari

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya fadi hanyoyin da Tinubu zai bi wajen samun nasara a jihar Bauchi.

Yakubu Dogara ya ce idan shugaba Bola Tinubu ya karasa aikin hako mai a tsakanin jihohin Gombe da Bauchi zai samu goyon bayan jama'a a 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng