Atiku Ya Zargi Tinubu da Son Sauya Shugabancin Majalisa da Karfin Mulki
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya soki mamayar da jami’an tsaro suka yi a Majalisar Dokokin Jihar Lagos a ranar Litinin
- Ya bayyana hakan a matsayin cin zarafin dimokuraɗiyya da kuma barazana ga tsarin mulkin Najeriya da APC ke ikirarin karewa
- Atiku ya bukaci a gudanar da cikakken bincike kan lamarin, yana mai cewa shugaba Tinubu ya fi dacewa da mayar da hankali kan gyara halin da ƙasa ke ciki
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi tir da yadda jami’an tsaro suka mamaye harabar Majalisar Dokokin Jihar Lagos.
Legit ta ruwaito cewa jami'an tsaro sun mamaye majalisar ne kamar yadda wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta ya nuna hakan.

Kara karanta wannan
Cacar baki ta balle tsakanin APC, NNPP kan yi wa gwamnatin Abba Gida Gida kishiya

Asali: UGC
Atiku ya wallafa Facebook cewa hakan cin zarafin dimokuraɗiyya ne kuma wani babban kuskure da ke iya jefa tsarin mulkin Najeriya cikin hadari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku ya bukaci bincike man mamayar majalisa
Atiku Abubakar ya bayyana mamayar jami’an tsaro a harabar Majalisar Dokokin Lagos a matsayin abin kyama da kuma ci gaba da take hakkin dimokuraɗiyya a ƙasar nan.
Ya ce abin mamaki ne yadda jami’an tsaron da ake zargin sun samu izini daga hukumomi su kutsa cikin majalisar don sauya shugabanci.
A cewarsa, ya zama dole a gudanar da cikakken bincike domin gano yadda aka yanke hukuncin tura jami’an tsaro domin kawo sauyin shugabanci a majalisar dokokin jihar.
Punch ta wallafa cewa Atiku ya ce:
"Wannan abu abin tir ne, kuma ya zama dole a yi bincike da gaggawa. Babu wata hujja da za ta iya halatta kutsen jami’an tsaro cikin majalisar da sunan warware rikicin shugabanci."
Atiku ya yi Allah-wadai da lamarin, yana mai cewa wadanda suka da'awar cewa su ne suka jagoranci fafutukar dawowar dimokuraɗiyya a Najeriya sune yanzu ke kokarin take ta.
Ya bayyana hakan a matsayin barazana ga dokokin dimokuraɗiyya da kuma cin fuska ga ‘yan Najeriya, musamman al’ummar jihar Lagos.
A cewarsa:
"Abin takaici ne a ce wadanda suka yi ikirarin fafutukar dimokuraɗiyya a baya su ne yanzu ke cin zarafin ita kanta dimokuraɗiyyar.
"Wannan ba kawai cin fuska ba ne, har ma barazana ce ga hakkin ‘yan kasa da zabin su."
Atiku ya ce duk wani rikici da ke faruwa a majalisar dokokin jihar ya zama wani al’amari da ke cikin tsarin dimokuraɗiyya.
A cewarsa, samun sabani a tsakanin ‘yan majalisa abu ne da aka saba da shi, amma amfani da jami’an tsaro domin tilasta sauyin shugabanci ba wani abu ba ne da ya dace da tsarin mulki ba.
Atiku ya yi kira ga Bola Tinubu
Atiku ya bukaci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, da ya mayar da hankali kan magance matsalolin da ke addabar kasar maimakon tsoma baki a harkokin jiha.
Ya ce yana da kyau a magance matsalar tattalin arziki, hauhawar farashi da matsin lambar da ‘yan Najeriya ke fuskanta maimakon shiga cikin rikicin majalisar jihar Lagos.
APC za ta ci zabe a 2027 - Uba Sani
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu zai yi nasara a 2027.
Uba Sani ya ce ayyukan da gwamnatin APC ke yi zai jawo mutane su zabi Bola Tinubu da sauran dukkan 'yan APC a jihar Kaduna.
Asali: Legit.ng