Fada Ya Barke Tsakanin Magoya Bayan APC da PDP, An Kashe Mutum 2
- Rahotanni sun bayyana cewa fada ya barke tsakanin magoya bayan jam'iyyar APC da PDP a jihar Osun, inda aka harbe mutane biyu
- 'Yan sanda da Amotekun sun kai dauki amma rikicin ya yadu zuwa wasu kananan hukumomi, inda aka hana APC shiga ofis
- Tsohon kakakin majalisar Osun, Timothy Owoeye, ya jagoranci APC domin shiga ofis a Ilesa ta Gabas, amma 'yan PDP suka hana su shiga
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Osun - An harbe mutane biyu a karamar hukumar Boripe ta jihar Osun a ranar Litinin yayin artabu tsakanin mambobin jam'iyyar APC da PDP.
Tashin hankalin ya samo asali ne daga takaddama tsakanin Gwamna Ademola Adeleke da ministan tattalin arzikin ruwa, Adegboyega Oyetola.

Asali: Facebook
An kashe mutane 2 a jihar Osun
Rigimar ta barke bayan kotun daukaka kara ta maido da shugabannin APC da aka kora, inda suka koma ofis suna murnar komawa kujerarsu, inji The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin da mambobin APC ke barin harabar majalisar, 'yan PDP suka tare su, lamarin da ya haifar da ya jawo hargitsi har aka harbe wasu mutane biyu.
Dakarun tsaro na Amotekun sun isa wurin, amma rahotanni sun ce mambobin APC sun ki amincewa da shiga tsakaninsu.
Yadda ta kasance a yankin Osogbo
A yankin Osogbo, mambobin APC sun mamaye sakatariyar karamar hukuma da ke Oke-Baale, inda daga bisani hadimin Gwamna Adeleke, Muniru Raji, ya kawo dauki.
An ce sakataren gwamnatin jihar, Teslim Igbalaye, ya jagoranci karin mambobin PDP don fatattakar APC daga sakatariyar karamar hukumar.
Ana zargin cewa an sake jiyo harbe-harbe yayin da bangarorin biyu suka sake gwabzawa a harabar majalisar.
An kashe mutum 1 a Osogbo
A Osogbo, an harbi mutum daya yayin artabu tsakanin mambobin APC da PDP a yankin karamar hukumar.
A Ife ta tsakiya, mambobin APC sun koma ofis, amma 'yan PDP suka fito domin nuna adawa, wanda ya haddasa cinkoso a hanyar Ibadan/Ikire.
A karamar hukumar Obokun kuwa, ana ci gaba da zaman dar-dar yayin da mambobin APC da PDP suka yi cirko cirko a kofar sakatariyar da aka rufe.
Rikici ya barke a Irewole, Ilesa, da Olurunda
A Irewole, mambobin PDP sun hana mambobin APC shiga ofis dinsu, inda suka tsaya a kofar sakatariyar don jiran ko ta kwana daga 'yan adawar.
Tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Osun, Timothy Owoeye, ya jagoranci komawar shugabannin APC a karamar hukumar Ilesa ta Gabas.
A Olorunda, an tura jami’an tsaro da dama don kare sakatariyar, yayin da kwamishinan raya karkara, Gani Olaoluwa, ke jagorantar mambobin PDP.
DSS ta mamaye zauren majalisar Legas
A wani labarin, mun ruwaito cewa, jami’an DSS da ‘yan sanda sun mamaye majalisar dokokin Legas a safiyar Litinin, 17 ga Fabrairu.
Haka kuma, an rufe ofisoshin shugabar majalisa, Mojisola Meranda, mataimakinta da sakataren majalisa, a cewar majiyoyi daga majalisar.
Wannan na faruwa ne bayan Mudashiru Obasa, tsohon shugaban majalisar, ya shigar da kara a kotu yana kalubalantar sauke shi daga mukaminsa.
Asali: Legit.ng