Siyasa: Sule Lamido Ya Yi Zazzafar Nasiha ga Malaman Izala da Darika
- Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya ce malamai sun fara rige rige da ‘yan siyasa wajen neman mulki a Najeriya
- Sule Lamido ya ce maimakon su zama jagorori, malamai sun koma yin kamfen da yin umarni ga mabiyansu kan wanda za su zaba
- Tsohon gwamnan ya yi gargaɗi da cewa rabuwar kai tsakanin malamai da rashin hadin kai a siyasa zai zama barazana ga kasa
- Wani malamin addini, Ustaz Kabiru Abubakar ya yi tsokaci kan kalaman Sule Lamido yayin da ya zanta da Legit
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Jigawa - Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya nuna damuwarsa kan yadda malamai ke kara shiga siyasa a Najeriya.
Sule Lamido ya ce wasu daga cikin shugabannin addini sun fara nuna fifiko a siyasa fiye da yadda ake tsammani.

Asali: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Sule Lamido ya bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo yayin ziyarar ta’aziyya ga Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun a Kaduna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Maganar Lamido kan shigar malamai siyasa
Sule Lamido ya ce malamai sun fara fitowa fili suna yin kamfen da umartar mabiyansu kan wanda za su zaba a siyasa.
Ya ce maimakon su zama masu ja-gora ga ‘yan siyasa, yanzu sun fara gwagwarmaya don samun mulki da kansu.
A cewarsa, idan malamai sun ci gaba da taka irin wannan rawa, ‘yan siyasa ba za su yi musu katsalandan ba, sai dai su tsaya su kalli abin da ke faruwa.
"Malamai sun gaza hada kai, a Izala akwai rikici, a Darikar Tijjaniyya akwai rikici, a Darikar Kadiriyya akwai rikici.
"Ya za a yi a ce 'yan siyasa su hada kai bayan malaman addini sun gaza hada kai,"

Kara karanta wannan
'Ba shi da tsoro ko kadan': Abin da Tinubu ya ce bayan babban rashin da Najeriya ta yi
- Sule Lamido
Barazanar rashin hadin kai ga Najeriya
Tsohon gwamnan ya ce kamar yadda jam’iyyun siyasa ke fama da rikice-rikice na cikin gida, haka ma kungiyoyin addini ke fama da rabuwar kai.
Ya gargaɗi cewa idan ba a hada kai ba, harkokin siyasa a Najeriya za su ci gaba da kasancewa cikin rudani da rikice-rikice.
Lamido ya ce ya kamata malamai su rike matsayin su na masu wa’azi da tsarkake al’umma, ba masu tayar da zaune tsaye a siyasa ba.
Ya bukaci a sami cikakken fahimta tsakanin bangarorin biyu domin kauce wa rikicin da ka iya tasowa a nan gaba.
Malamai sun taka rawa a siyasar 2023
A zaben 2023, malamai sun taka rawa sosai wajen kiran mabiyansu su fito su yi rijistar zabe da kada kuri’a.
An samu wasu limamai da fastoci da suka fito fili suna goyon bayan wasu ‘yan takara a hudubobinsu.

Kara karanta wannan
Mutumin da Tinubu ya naɗa a muƙami ya tsallake rijiya da baya, an yi yunƙurin kashe shi
Wasu limamai sun bukaci jama’a su zabi shugabanni bisa la’akari da addini, yayin da wasu fastoci suka yi irin haka a wuraren ibada.
Legit ta tattauna da malamin addini
Wani malamin addini a jihar Bauchi, Ustaz Kabiru Abubakar ya bayyanawa Legit cewa wasu kalaman Sule Lamido ba su dace ba.
Malamin ya ce:
"Rabuwar kai a tsakanin malamai ya bambanta da rabuwar kai a tsakanin 'yan siyasa.
'Abu ne sananne a samu sabani a tsakanin malamai shekaru sama da 1,000 da suka wuce. Saboda haka ba hujja ba ne 'yan siyasa su ce za su yi la'akari da haka"
Uba Sani ya ce APC za ta yi nasara a 2027
A wani rahaton, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya ce jam'iyyar APC na cigaba da samun karbuwa a tsakanin 'yan Najeriya.
Gwamna Uba Sani ya ce bisa karbuwar da jam'iyyar ta ke, shugaban kasa Bola Tinubu zai yi nasara a zaben shugaban kasa na 2027.
Asali: Legit.ng